TAMBAYA TA 121


TAMBAYA 1,720
As salamu aleykum dafatan an shan ruwa lahia.malan wani ne ni chema babu "taala"tikin sallama misali: as salamu aleykum waramatullahi taala wabarikatihu to chine yatse inkawo hujadda baagayi hakanan
AMSA
 waɗannan lafuza da aka ambata idan zakayi wa mutum sallam sune kace "assalamu alaikum" (waɗannn shine bayanin da Imamun Nawawi yayi a cikin sharhin sahihu muslim juz'i na 9 shafi na 172 inda yake sharhin hadisi na 2841).
Sannan wanda yace:
 - "assalamu alaikum"yana da lada goma (10), bukhari ne ya rawaito a cikin Adabul mufrad hadisi na 987
- "assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuhu" yana da lada talatin (30)
- "assalamu alaikum wa rahmatullahi a barakatuhu wa magfiratuhu" yana da lada araba'in (40) hadisin na cikin Assahiha na Albani hadisi na 1449
- "salamun alaikum" kamar yanda yake cikin suratl Ra'ad Aya ta 24.
- sannan za ka iya sallama sai ka haɗa da sunan mutum kaman yanda Allah yayi wa Annabawansa sallama tare da sunansu, kamar inda Allah yace "salamun ala Nuhin fil Alamin" suratul Saafat aya ta 89, da "salamun ala ibrahin" suratul Saafat aya ta 109, da kuma "salamun ala musa wa harun" suratul Saafat aya ta 120. 
Don haka dukka waɗanna hanyoyin salama sun halatta a musulunci.
Waɗannan bayanai na cikin: fathul baari sharhin sahihul bukhari na ibn hajar juz'i na 6 shafi na 535, sharhin sahihu muslim na uthaimin juz'i na 8 shafi na 149, da sharhin muwaɗɗa ta uthaimin juz'i na 1 shafi na 310, da ibnul qaiyim a cikin zadul ma'ad juz'i na 2, da tahrirul kalam fi masa'ilissalam na Abu Rufaida.
Wallahu aalam
Amsawa: Mal Adam Daiyabu
Post a Comment (0)