MAGANIN ƘURAJEN FUSKA

MAGANIN KURAJEN FUSKA


A samu leman tsami a rika gogawa a fuska za'aji suna zafi to yana kashe kurajen ne. Ko kuma a samu karas ko dankali a rika shafawa insha Allah za a dace....

Sannan idan sunyi tabo ayi daya daga cikin wannan inshaa Allah xasu bace..

· A samu ganyen dogonyaro, sai a hada shi da kurkur, sannan sai a shafa a fuska. A jira tsawon minti 15, sannan a wanke da ruwan dumi.

· Za a iya shafa markadadden dankalin Turawa a kan tabo. Hakan na magance kurajen fuska, sannan ya hana su sake fitowa.

· A daka tafarnuwa sai a shafa a kan tabo. Tafarnuwa tana wari, amma tana gyara fuska, sannan ta magance tabon fuska.

· a hada karas da tafarnuwa da zuma sai a shafa a fuska na tsawon minti 20 kafin a wanke.

· A samu hodar ‘baking soda’, sai a hada ta da ruwa, sannan a shafa a fuska zuwa minti 2 ko 3, daga nan a wanke fuska da ruwan dumi.
Post a Comment (0)