TUSHE DA ASALIN HAƘURI SAI MACE

TUSHE DA ASALIN HAKURI SAI MACE



Duk fadan mace tana da hakuri da juriya,eh Ina da hujjar fadin hakan.

Idan mace ta dau ciki daga wata daya har zuwa hudu cikin wahala da laulayi take wata ma har ta haihu babu laifiya,amma jeki duba Gaddafi idan yayi sati yayi yana malaria Sai ya zama abin tausayi.

Idan tazo nakuda wata har Dan ya fita bata hayyacin ta wata kuma ta karu Sai an mata dinki,ga bakar azaba da budewar Kashi,duk ita kadai,amma dubi malam inusa idan yaje toilet yana basir😏.

Wata anan zata Sami hawan jini wata buguwar jini amma duk da haka abinda zai sanyaya mata Rai a wannan lokacin shine kukan da jaririn zai yi na farko.

Ko kasan zafin da uwa take Sha a lokacin da jaririn ta ta kama nononta na farko domin sha??amma duk da wannan zafin hakan ba zai hana ta bashi ba gudun kada yayi kukan yunwa.

Da zarar da ya fara hakori,haka zai Kama kan nonon ya ciza amma duk da haka murna zata dinga yi tana nunawa jama'a kan dan ta yayi hakori.

Tana cin abinci,barci take ko kuwa cikin taro take haka zai yi fitsari ko kashi dole ta yanke abinda take taje ta wanke mishi.

Ya girma yayi wayo haka zai dinga barar mata da kaya yana mata barna amma ita ba wannan bane damuwar ta,damuwar ta shine kada yaje ya janyo abinda zai cutar dashi.

  Amma wai duk da haka mace itace abin wulakantawa itace abin tozartawa,wani ma uwar shi na fada yana fada idan baka tausayawa mace ba ka mutunta to baka da amfani.

Uba karfin shi yake baka amma ita uwa lafiyar ta take baka Dan haka mace ta zarce duk yadda kake tunani idan ka mutunta ta wani zai mutunta taka uwar idan ka tozarta wani zai tozarta taka.

   Ya Allah duk wanda baya tausayawa mace Allah ka hadashi da cinnaka mara tausayi yayi ta gannawa Dan banza cizo😏😏😏😏
Post a Comment (0)