TAMBAYA TA 119

TAMBAYA 1,719
Aslm malam ina wuni ya azumi tambayanashine Dan Allah mehukuncin Wanda yake kallo a azumi
AMSA
Illar kallon fina finan wato drama ga kaɗan daga cikin illolinta :
1. Ɓata lokaci wanda kuma Allah zai tambayemu akan duk wani sacond ɗaya na rayuwarmu
2. Kallon tsaraici don irin tufafin da matan suke sakawa yana nuna tsaraici don bada hijibi ajinkinsu suke finifinan ba
3. Ɓata tarbiya don yara ƙanan na koyan soyayya a ciki wanda kuwa koda lokacin yinsu baiyi ba
4. Kallonsu yana sa a fitinu dasu, wanda yakan sa wani yayi sha'awarsu ko har ta kai daya ce zai gwada nemansu.
5. Hana mata zaman aure, ta hanyan koyan salon da zasu iya dinga kashe aurensu
6. Mace ta bar garinsu babu muharrami domin tafiya yin wani fage, to irin wannan da ta saɓawa Allah me zata koya miki
7. Akwai Jin waƙa a cikin fim ɗin wanda kuma jin waƙa haramun ne
8. Kallon taimakekeniya ne akan ɓarna ne da saɓo wanda kuma Allah ya hana mu
Gaskiya bisa wannan abubuwa na haramci da kallon finafinan hausa ya ƙunsa ana iya ace masa shima haramun ne.
Wallahu aalam
Amsawa: Mal Adam Daiyib

Post a Comment (0)