TAMBAYA TA 86


Tambaya
:
Shin ko ya halatta mai sallar farilla yayi koyi da mai sallar nafila ko kuma akasin haka:??
:
Amsa
:
Alal-haƙiƙa wannan wata mas'alace da
Malamai sukayi saɓani a kanta, magana ta farko daga cikin maganganun da Malamai sukayi itace:
:
Mazhabin SHAFI'IYYA da kuma HANABILA sun tafi ne a kan cewa ya halatta mai sallar farilla yayi koyi da mai sallar nafila, daga cikin dalilansu sun kafa hujja da wannan Hadisi na Mαnzon Allαh(ﷺ) wanda bayan sun idar da sallar Asubah sai Mαnzon Allαh(ﷺ) yaga waɗansu mutane guda biyu a gefe ba suyi sallah tare da su ba, sai ya tambayesu meye ya hana ku kuyi sallah tare da mu? Sai sukace ai mun riga munyi sallarmu ne tun a gida, sai Mαnzon Allαh(ﷺ) ya ce da su:
:
"فلا تفعلا، إذا صليتما في رحالكما ثم أدركتما الإمام ولم يصل فصليا معه، فإنها لكما نافلة"
(رواه أبو داود)
MA'ANA:
Kada ku sake yin irin haka, nan gaba idan kuka riga ku ka yi sallarku a gida kuma sai ku ka zo ku ka riski Liman a Masallaci ba su yi sallah ba, to kuyi sallah tare da shi, ita wacce kuka sallata tare da Liman ta zama nafila a gare ku,
:
Sannan su ka ce Ma'azu Ɗan-Jabal ya kasance yana zuwa Masallacin Mαnzon Allαh(ﷺ) a yi sallar Isha'i da shi, daga nan kuma sai ya koma unguwarsu kuma dama shine Liman a can, mamu suna jiransa yaje yayi musu sallar Isha'i, haka Ma'azu Ɗan-Jabal ya kasance ya na yi kullum kuma Mαnzon Allαh(ﷺ) bai hanashi ba, tare da cewa shi sallar da yake yi musu limancinta a matsayin nafila ta ke a wajensa tunda ya riga yayi tasa tare da babban Liman wato Mαnzon Allαh(ﷺ).
:
Magana ta biyu itace: Mazhabin MALIKIYYA da kuma HANAFIYYA sukace ba ya halatta mai allar farilla yayi koyi da mai sallar nafila, su kuma daga cikin dalilansu sun kafa hujja da Hadisin Mαnzon Allαh(ﷺ) da ya ke cewa:
:
"إنما جعل الإمام ليؤتم به، فلا تختلفوا عليه، فإذا ركع فاركعوا……………"
(رواه البخاري ومسلم)
MA'ANA:
Haƙiƙa an sanya Liman ne dan (ku mamu) kuyi koyi da shi, kada ku saɓa masa, idan yayi ruku'u kuma sai kuyi……
:
Sukace idan mai sallar farilla ya bi mai sallar nafila to haƙiƙa ya saɓawa Liman a wajen niyya, danhaka ba zai yi koyi da shi ba, To amma sai dai Malaman da suka tafi akan cewa ya halatta ayi sukace wannan Hadisi da Mαnzon Allαh(ﷺ) ya ce kada a saɓawa liman yana Magana ne a kan kada a saɓa masa ne a cikin ayyukan sallah, shi yasa ma a cikin Hadisin yace kada kuyi ruku'i har sai Liman yayi, kada ku ɗago daga ruku'i har sai Liman ya ɗago,
:
Danhaka magana mafi Inganci itace ya halatta mai sallar farilla yayi koyi da mai sallar nafila ko kuma akasin haka, sannan ya halatta mai sallar farilla yayi koyi da mai sallar farilla ko da kuwa nau'in sallolin sun bambanta da juna,kamar mai sallar azuhur yayi koyi da mai sallar la'asar, ko kuma mai sallar ramuwa yayi koyi da mai sallar lokacinta ko kuma akasin haka, Malamai sukace duk Ya halatta a yi hakan:
:
※(шαʟʟαнυ-тα'αʟα α'αʟαмυ)※
:
▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂
              Daga Zaυren
             Fιƙ-нυl-Iвadaт
▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂
           Mυѕтαρнα Uѕмαи
              08032531505
▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂
Doмιɴ ѕнιɢα ѕнαғιɴмυ dαкє ғαcєвooк ѕαι αѕнιɢα wαɴɴαɴ lιɴк кαwαι αyι ""lιкє""👇🏾
:
https://m.facebook.com/fiqhul.ibadat/
Post a Comment (0)