WASU ABABEN LURA A YAYIN NAZARIN TARIHI 3


WASU ABABEN LURA A YAYIN NAZARIN TARIHI
Kabir Abubakar Asgar

Fitowa Ta Uku

B. RIKICI TSAKANIN (AQARAN) SA’ANNI

Allah cikin iko da buwayarsa bai taqaita falalarsa ga mutum guda a wani zamani ko waje. Shi kuwa dan adam yana da son a ce shine a saman sauran tsararrakinsa. Wannan shi yake jawo gasa da cin dunduniya da qoqarin ganin bayan abokin hamayya. Don haka, duk inda sa’anni suke a wata sana’a ko kasuwanci ko siyasa ko ilimi ba ka rasa irin matsalolin hassada da yarfe da raini da mummunan fata da makamantansu. A duk lokacin da wani yai fice a tsakanin tsararrakinsa sai ka ga sauran wadanda suke ganin sun cancanci irin wannan matsayin suna yi masa gani-gani. 

A duniyar malanta abin ya fi tsanani, wataqila saboda su malamai suna da baki da alqalami kuma wasuns sukan gayyato mabiyansu su taya su wannan badaqala, ko ma ace, uwa-uba wasu kan mai da fadan kamar aqida. Watakila mai karatu zai yi mamaki in ya ji cewa malamai cikin magabata na kwarai an ruwaito cewa wasunsu sun auka cikin tasirin dabi’a ta wannan fuskar. Alal misali tsakanin Qatada da Yahya Bn Abi Katheer da tsakanin Maliku da Ibn Abi Zi’ib haka nan tsakanin Assha’abiy da Ikrimah. Sai kuma Ibrahim Annakha’iy da Sha’abiy da kuma Abu Yusuf Al-Qadiy da Muhammad Bn Alhassan Asshaibaniy. Haka muma Ibn Mandah da Abu Nu’aim Al-Asfahaniy da kuma Ibn Sa’id da Ibn Abi Dawud. Sai kuma tsakanin Abu Hafs Al-Fallas da Muhammad Bn Hatim Al-Marwaziy. Daga baya-bayan nan rikici ya taba yin qamari tsakanin Ibn Hajr da BadrudDeen Al-‘Ainiy. Haka kuma tsakanin Suyutiy da Sakhawiy.

Wani labarin rikicin mai ban mamaki tsakanin tsararraki ya faru a makarantar Shafi’iy. Lokacin da ciwon ajali ya kama shi sai ya ce Abu Ya’aqub Al-Buwaitiy ne zai gaji kujerata, sanadiyyar haka su Al-Muzaniy da Abubakr Al-Asam da Harmala da wani cikin ‘ya’yan Shafi’in suka qullace shi. Hasali ma sun taba yi masa sharrin da sai da hukuma ta kama shi. Shi kuwa Ibn AbdulHakam zuciya ya yi ya bar makarantar ya je ya kafa ta shi.  

Saboda haka masana tarihi suna jan kunnen mai karatu sosai akan ya lura da kyau wajen mu’amalantar maganganun tsara ko kini akan tsaransa.

Ban san wanda ya kai Zahabiy kwarewa akan iya tantance maganganun da suke nuni izuwa ga cewa mai su ya yi su ne kawai don ya biya buqatar zuciyarsa ba. Har ila yau, maganganun da Zahabiy ya yi a wurare dabam-dabam game da wannan matsala in aka kalle su za su ba da sakamakon cewa: Asali ba a son ruwaito maganganu na batanci da wani ya yi akan abokin hamayyarsa. In kuma har ya zama dole a hakaito maganar sa to dole ne a fadakar akan cewa wannan magana fa akwai alamar son zuciya ko zalunci a cikinta. Amma ana iya karbar maganar in ta bayyana cewa ba son zuciya a ciki, kamar idan an samo irinta daga wasu wadanda su ba a san suna da husuma tsakanin su da wanda ake magana akai ba.

(To be continued)
Post a Comment (0)