JA'IRI
Shugabanci ya yi
Mulki kam ya yi
Hawa karaga ya yi
Juya mutane ya yi
Sharholiya ma ta yi.
Tsula tsiya na da daÉ—i
Shegantaka tana da daÉ—i
Samartaka na da daÉ—i
Waye yau za ya hanani
In sheƙe ayata.
In bi mata a layi
In na so in busa sigari
In bugi kowa cikin gari
Ina nan sai garari
Babu mai tankani.
Ni kuma gani da ƙarfi
Kuma bana son raini
A yanzu in ka kula ni
Aradu ka sha kaifi
Kuma dole a barni.
Har suna aka sauyan
Audu a da akan kiran
Ja'iri yau ake kira
Audu da za ran ka kiran
Yanzu ba mai ganewa.
Tafiya yau tai nisa
Ina ta zancen zuci
In na zamo mamaci
Waye zai yi takaici
Da mutuwar ja'iri.
Kuma fa za a sa ni kabari
Na ji ana ta labari
Wai akwai Walakiri
Da guduma a kabari
Yana bugu da ƙarfi.
Kai Allah dai ya shirya
Ka azamu bisa hanya
Mu zamo abin koyi
Da ƙamshi ba ɗoyi
Kuma babu fariya.
#haimanraees