YADDA AKE WARWARE MATSALOLIN RAYUWA

YADDA AKE WARWARE MATSALOLIN RAYUWA 
:



*TAMBAYA*❓
:
Assalamu alaikum Dafatan Malam ya tashi lafiya,.wata ‘yar uwa ce take son Karin bayani a kan wani lamari wato ya kasance tana da aminiya sai take gaya mata matsalolnta sai ta hadata da wani Dan uwanta malami akan zai bata addu’oi, sai ta ce tana so kuma ya mata istihara sai su kaje sai ya yi istharan, a lokacin ya mata bayani kamar yadda tayi wa kawarta bayani har ya karbi kudin da za’a yanka kaza saboda za’a karanta suratul yasin. Malam sai yabata rubutu yace ta sayi tumbin shanu ta dafa da rubutun. Ta kuma yi amfani da kifiya ta naci daidai ta roki Allah ya kareta daga sharrin makiya, so daga baya tai ta tambaya aka ce taguji irin wadannan malaman, har tazo ta karyata abin. To mal ya matsayinta yake?
:
*AMSA*👇
:
Wa’alaikum assalam Akwai alamun da suke alamin ba mai ilimi bane, don haka Ina bata Shawarar da ta rabuda shi don kar ta fada cikin halaka. Ana iya samun waraka daga matsaloli ta hanyar yawaita istigfari da tuba zuwa ga Allah da mayar da hakkokin da ba na ka ba, da yawaita sadaka, da nisantar cin mutuncin mutane, da yawaita addu’o’i, saboda addu’a tana tunkude bala’i, taimakawa mutane da yaye musu bakin ciki na daga cikin abubuwan da suke warware mushkiloli, Annabi (SAW) Idan abubuwa suka dame shi yana ta shi izuwa sallah kamar yadda Abu-dawud ya rawaito shi kuma Albani ya inganta shi a hadisi mai lamba ta: 4171> Gano ainihin matsala da shawartar masana wadanda suka goge a rayuwa yana taimakawa wajan warware wasu matsalolin, mutukar shawarar da suka bayar bata sabawa ka’idojin sharia ba, ana iya samun mafita in aka bita.

Allah shine mafi Sani.

Ku kasance damu cikin wannan group domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
WHATSAPP👇 
https://wa.me/+2348087788208

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚَ
Post a Comment (0)