WASU ABABEN LURA A YAYIN NAZARIN TARIHI 5


WASU ABABEN LURA A YAYIN NAZARIN TARIHI

Kabir Abubakar Asgar

Fitowa ta Biyar

D. KO TARIHI NA MAIMAITA KANSHI?

Fadin cewa ‘tarihi na maimaita kanshi’ magana ce shahariyya a bakin mutane. Abu ne mai sauki a fahimci cewa maganar ta dade kuma ta shiga cikin al’ummomi mabambamta da yarurruka dabam-dabam.

Abin da maganar take nufi shine duk abin da kake gani yana faruwa a rayuwa ta fuskar siyasa da tattali da yaqe-yaqe da daukakar dauloli ko faduwarsu da samuwar damuwoyi dabam-dabam a al’ummar dan adam ko cututtuka ko annoba ko fari da yunwa da kuma fadi-tashin da dan adam yake yi don raya qasa da gyara ta da inganata rayuwarsa a bayan qasa da gwagwarmayar neman ‘yanci ko mulki ko faruwar rikici tsakanin qasashe ko tsakanin ra’ayoyi dabam-dabam da sauransu to ba wanda ba a taba ganin makamancinsa ba a can baya.

Fadin haka ya samo asali ne daga kasancewar dabi’ar dan adam ba ta canzawa, shi ya sa ake samun maimaituwar abubuwan da ke faruwa a kodayaushe. Masana da yawa na iqirarin cewa su gano cewa, kamar yadda rayuwar mutum ke jujjuyawa tun daga haihuwa izuwa yarinta da girma sannan kuma tsufa da mutuwa to haka ma duniyarsa take jujjuyawa.
In muka yi la’akari da fadin Allah (SWT) game da cin nasara ko rashinta a yaqi cewa (Haka muke jujjuya [nasara ko rashinta] a yaqoqi tsakanin mutane [Alu Imran, 140]), za mu ga cewa, duk da ayar ta zo ne don bayani akan halin yaqi, za a iya fadada ma’anar abin da tai ishara na maimaituwar nasara ko rashinta da canjejeniyar hakan tsakanin rundunoni biyu dake gwabza yaqin. 

Baya ga haka, malaman Tarihi da dama irin su Ibn Khaldun da Arnold J. Toynbee da Niccolo Machiavelli Da Mark Twain G. W. Trompf da makamantansu sun tattauna wannan batu tare da kawo misalai na qaidojin da ke tabbatar da aukuwar maimai din a tarihin dan adam.   
 
Alal misali, Niccolo Machiavelli, a lokacin da yake bayani akan daular Florentine ya zayyana wannan qa’ida kuma ya alaqanta ta da tashi da faduwar dauloli a matsayin misalin tarihi da yadda yake maimaita kansa inda ya ce: “Duk wanda yai la’akari da jiya kuma ya kalli yau kai tsaye zai gane cewa birane da mutane ba su taba canzawa daga dabi’arsu ba. 

Saboda haka yana da sauqi a yi amfani da hanyoyin da mutanen da suka bi don maganin matsalolinsu wajen maganin matsalolin yau…..[sannan kuma a fahimci cewa] da zaran daula ta kai qololuwar qarfinta, ba da jimawa ba za ka ga ta fara kama hanyar karyewa…” .
 
Shi kuwa G. W. Trompf a littafinsa mai suna ‘The Idea of Historical Recurrence in Western History’, bin sawun yadda akai ta samun maimaituwar abubuwan da ke faruruwa a fagen siyasa a yammacin Turai yayi a tsawon dubban shekaru. Sannan ya tuqe izuwa ga cewa, in har akwai wani darasi da za a dauka daga Tarihi to babu kamar sanin cewa abubuwan da ke faruwa a tarihin maimai ne, don haka jiya tana bamu satan amsar abin da ka iya faruwa yau, sannan kuma ta ba mu dammar tunani da tsara rayuwar gobe.

(To be continued)
Post a Comment (0)