RUFE MASALLATAI SABODA ANNOBAR CORONAVIRUS


RUFE MASALLATAI
 
SABODA ANNOBAR KORONA

Rubutawar
Abdulmajid Muhammad Umar

22/Ramdana/1441
Birnin Madina, KSA
 
Da sunan Allah Mai rahama, Mai jin kai.
GABATARWA
Godiya ta tabbata ga Allah, tsira da aminci su tabbata ga Annabi Muhammad SAW da alayensa da sahabbansa gaba daya.
Bayan haka, hakika duniya ta samu kanta a wani yanayi wanda ya canja abubuwa da yawa; na addini da rayuwa.
Duk da cewa malamai a wannan zamani sunyi sabani akan hukucin rufe masallatai, hakan bai hana a yi rubutu kan hukucin hakan a ilmance.

KAFIN NA TSUNDUMA CIKIN AINIHIN BAYANI KAN RUFE MASALLATAI, AKWAI WASU MUHIMMAN GINSHIKAN DA YA KAMATA MAI KARATU YA SANI;
Allah Ya kara mana fahimta, Ya ba mu kirji mai yalwa, Ya kara mana sani a addini, Ya nuna mana gaskiya gaskiya ce, Ya ba mu ikon bin ta, Ya nuna mana karya karya ce Ya ba mu ikon guje mata.

Na Farko: A Musulunci akwai hukunce-hukunce da suke banbanta tsakanin daidaikun mutane ko wani bangare na mutane da kuma gaba daya al’uman gari ko kauye; misali: 
Misali Na Farko: Kiran sallah ba wajibi ba ne a kan kowa, amma idan al’umuman gari suka ki kiran salla to za a iya yakarsu a kan haka, shi ya sa Annabi SAW a hadisin (Bukhari 610) da (Muslim 382) idan ya tafi jihadi yakan jira har sai lokacin kiran sallar asubahi, idan ya ji an kira salla a gari sai ya dakatar da afkawa mutanen, Imam al-Bukhari ya sawa babin suna:
 بَابُ مَا يُحْقَنُ بِالأَذَانِ مِنَ الدِّمَاءِ (Babin da Kiran Sallah ke Hana Zub da Jini). 
Misali Na Biyu: Idan mutun daya ko wasu mutane suka hana zakka ba a yakar su, amma idan mutanen gari gaba dayansu suka hana zakkah za a yake su, shi ya sa Sayyiduna Abubakar ya yaki al’ummar da suka hana zakkah bayan rasuwar Annabi SAW.  
Misali Na Uku: Sallar idi a kan kowane mutun ko wata unguwa ba wajibi ba ce, amma a kan al’umar gari wajibi ce su yi sallar idi ko da a masallaci daya ne.
Misali Na Hudu: Sallar dare a Musulunci a cikin watan Ramadan (Tarawihi ko Tahajjudi) ba wajibi ba ce a gida ko a masallaci, amma wajibi ne a cikin al’uma a samu masu yi ko da masallaci daya ne a watan Ramadan, kamar yadda Ibn AbdilBar ya kawo a littafinsa at-Tamhid 8/119. 
Misali Na Biyar: Sallar jam’i a masallaci sunnah ce mai karfi a wajen mafi yawan malamai dangane da daidaikun mutane, amma babu sabani a kan wajibi ne al’umar gari su samar da sallar jam’i ko da a masallaci guda daya ne.
Abin da zai tabbatar da haka shi ne Ibn AbdulBarri ya hakaito ijma’in malamai a kan haramcin rufe masallatai a littafinsa (At-tamhid 18/333), haka nan Ibnu al-Qaddan (al-Iqna’ fi Masa’il al-Khilaf 1/ 145). 
Kuma Annabi SAW ya ce: Babu wasu mutum uku a gari ko a kauye da ba sa yin sallar jam’i face sai Shaidan ya gallabe su. (Abu Dawud hadisi 547).

Wannan Ka’ida ce muhimmiya a sharia; duk abin da a ka ce maka ba wajibi bane, to a na magane galibi ga daidaikun mutane, ba hukunci bane na dukkanin al’umma a jumlace: kamar yadda Imam Ash-Shadibi ya ce: 
إِذَا كَانَ الْفِعْلُ مَنْدُوبًا بِالْجُزْءِ كَانَ وَاجِبًا بِالْكُلّ؛ كَالْأَذَانِ فِي الْمَسَاجِدِ الْجَوَامِعِ أَوْ غَيْرِهَا، وَصَلَاةِ الْجَمَاعَةِ، وَصَلَاةِ الْعِيدَيْنِ، وَصَدَقَةِ التَّطَوُّعِ، وَالنِّكَاحِ، وَالْوِتْرِ، وَالْفَجْرِ، وَالْعُمْرَةِ، وَسَائِرِ النَّوَافِلِ الرَّوَاتِبِ؛ فَإِنَّهَا مَنْدُوبٌ إِلَيْهَا بِالْجُزْءِ، وَلَوْ فُرِضَ تَرْكُهَا جُمْلَةً لَجُرِّحَ التَّارِكُ لَهَا, أَلَا تَرَى أَنَّ فِي الْأَذَانِ إِظْهَارًا لِشَعَائِرِ الْإِسْلَامِ؟ وَلِذَلِكَ يَسْتَحِقُّ أَهْلُ الْمِصْرِ الْقِتَالَ إِذَا تَرَكُوهُ، وَكَذَلِكَ صَلَاةُ الْجَمَاعَة. الموافقات (1/ 211).

Abu Na Biyu: ba fa yanzu aka fara munanan annobobi ba a tarihi, an yi annobobi a zamunan baya tun daga zamanin annabi da zamanin sahabbai, ga misalai; 
Misali Na Farko: Annabi ya zo Madina ya same ta tana fama da annoba; Sayyiduna Abubakar da Bilal da wasu sahabbai sun yi rashin lafiya mai tsanani har wasu ma sun dauka za su mutu sakamakon wannan annoba, hadisin na cikin (Bukhari 1889), a ciki har Nana Aisha take cewa: A lokacin Madina ita ce mafi fama da annoba a ban kasa, (وَقَدِمْنَا المَدِينَةَ وَهِيَ أَوْبَأُ أَرْضِ اللَّهِ) amma ba a rawaito mutuwa ba a lokacin. 
Misali Na Biyu: A Madina a zamanin Sayyidina Umar an yi annoba wadda Bukhari (2643) ya rawaito: Abul Aswad ya ce; na shigo Madinah ana annoba ( وَهُمْ يَمُوتُونَ مَوْتًا ذَرِيعًا) mutane barkatai na mutuwar faraddaya. kamar yadda Ibn al-Jauziy ya fassara ya ce: والذريع: السَّرِيع الْكثير (Kashfu al-Mushkil, 1/ 126).
Misali Na Uku: An yi annoba a zamanin Sayyidina Umar a shekara ta 18 a kasar Shaam wanda ita ma ta yi tsanani kwarai da gaske, Abu Ubaida shi ne shugaba ya tara mutane ya musu jawabi daga baya sai ya rasu, aka nada Mu’az bin Jabal shi ma ya tara mutane ya musu nasiha, daga baya sai ya rasu, adadi mai yawa na sahabbai suka rasu, kamar yadda Bukhari (5728) ya rawaito wani bangaren labarin.
Ibn al-Athir a cikin (al-Kamil 2/337) ya kara da cewa; sahabin Annabi SAW Amr bin Aas ya dibi mutane sun hau saman dutse, kuma daga nan Allah yaye musu.
Misali Na Hudu: An yi annoba a birnin Basra shekara ta (64) ta tsawon kwanaki hudu kacal, wanda a cikin kwana ukun farko; mutun dubu dari biyu da sha hudu suka rasu (214,000) a kwana na hudu kuma galibin mutanen garin suka mutu. Kamar yadda Ibn al-Jauzi ya kawo cikakken labarin a littafinsa al-Muntazam (6/25) da sauransu malamai da dama. (wadannan misalan duka sun faru ne a rayuwar sahabbai).

Abu Na Uku: Tarihi ya ga mace-mace wadanda suke firgitarwa, don ya gabata an yi annoba da ta taba kisa a cikin gari daya (Basra), da ba a taba ganin irin haka ba a wannan zamani namu. (a ce mutun sama da dubu dari biyu (200,000) sun rasu a kwana uku). 

Abu Na Hudu: Yaduwar annoba ta hanyar cakuduwa tsakanin mai cuta da mara cuta ba sabon abu ba ne, Annabi SAW ya tabbatar da wannan a hadisai; a Bukhari hadisi na (5771) Annabi SAW ya ce: "kada a sake a hada mara lafiya da mai lafiya”.
 «لاَ يُورِدَنَّ مُمْرِضٌ عَلَى مُصِحٍّ »
A Bukhari akwai hadisi na (5707) wanda yake magana a kan guje wa mai cutar kuturta, Annabi ya ce: (وَفِرَّ مِنَ المَجْذُومِ كَمَا تَفِرُّ مِنَ الأَسَدِ). "Ka guje wa kuturu kamar yadda yake guje wa zaki".
A wani hadisin na Bukhari (5728), Annabi SAW ya ce: idan kuka ji labarin annoba a gari kada ku shiga, idan kuma kuna ciki kada ku fita. 
«إِذَا سَمِعْتُمْ بِالطَّاعُونِ بِأَرْضٍ فَلاَ تَدْخُلُوهَا، وَإِذَا وَقَعَ بِأَرْضٍ وَأَنْتُمْ بِهَا فَلاَ تَخْرُجُوا مِنْهَا»
Shi ma abin da ake fahimta shi ne ana iya daukar cuta ta hanyar haduwa da cakuduwa.

Abu Na Biyar: Akwai hanya ta yaduwar annoba da Annabi SAW ya tabbatar da ita, kari a kan cudedeniya; a hadisin Muslim, hadisi na (2014) Annabi ya ce: "ku rufe kwanukanku da abin shanku, domin a duk shekara akwai wani dare da annoba ke sauka, babu wani kwano da abin shan ruwa da ke bude face wannan annoba ta fada a cikinsa. 
)غَطُّوا الْإِنَاءَ، وَأَوْكُوا السِّقَاءَ، فَإِنَّ فِي السَّنَةِ لَيْلَةً يَنْزِلُ فِيهَا وَبَاءٌ، لَا يَمُرُّ بِإِنَاءٍ لَيْسَ عَلَيْهِ غِطَاءٌ، أَوْ سِقَاءٍ لَيْسَ عَلَيْهِ وِكَاءٌ، إِلَّا نَزَلَ فِيهِ مِنْ ذَلِكَ الْوَبَاءِ( 
Abu Na shida: Lalura ana amfani da ita ne iyakacin gwargwadon ta, ba a kari kuma a ce wai ai lalura ce.
Sannan ba ya halatta a sarayar da duk wani abu da za a iya yin sa, ma’ana; abin da zai iya yiwuwa, ba a watsar da shi saboda wannan ba zai yiwu ba. Misali; wanda ba zai iya tsayuwa a sallah ba amma zai iya yi a zaune, an yi masa rangwame ya yi salla a zaune, a kan haka, bai halatta ya yi amfani da wannan rangwamen ba ya yi sallar a kwance, ko ma ya bar sallar gaba daya, kamar yadda Hadisi ya nuna; (Bukhari 1117). 
«صَلِّ قَائِمًا، فَإِنْ لَمْ تَسْتَطِعْ فَقَاعِدًا، فَإِنْ لَمْ تَسْتَطِعْ فَعَلَى جَنْبٍ»

Abu Na Bakwai: Manzon Allah ya yi Salatul Khaufi tare da sahabbai adadi mai yawa a yakuna daban-daban, a cikin littattafan hadisi na kusa (Muwadda, Bukhari, Muslim da sauransu) akwai salo-salo na wannan sallar akalla guda (7), Imam al-Nawawi ya hakaito nau’uka (16) a cikin (Al’muj’mu 4/407), kai har ma magana ya halatta mutun ya yi wa dan'uwansa a cikin sallar ya ce a misali; Ga wani kafiri nan kusa da kai.

Abu Na Takwas: Neman magani da kauracewa mai cuta a Musulunci halal ne ko mustahabbi, kuma Annabi SAW ya kwadaitar a kan neman magani kuma shi ma ya yi magani, ya kuma ba da magani, amma ba wajibi ba ne, ma’ana wanda ya ce bai da bukatar shan magani ko nemansa bai yi laifi ba; Ibn Taimiyya yana cewa: (kwata-kwata neman magani ba lalura ba ne, kuma ban san wani mutum daya daga cikin magabata ba da ya wajabta shi) (al-Fatawa al-Kubra 1/ 389).
      (فَثَبَتَ بِهَذَا أَنَّ التَّدَاوِيَ لَيْسَ مِنْ الضَّرُورَةِ فِي شَيْءٍ...وَلَسْت أَعْلَمُ سَالِفًا أَوْجَبَ التَّدَاوِي) 
Imam al-Nawawi yana cewa: (Za a dauki umarnin da aka yi dangane da kaurace wa mai kuturta a kan abu ne da ake so, amma dai ba wajibi ba ne). (Sharhin Muslim; 14/ 228)
 (وحمل الأمر باجتنابه والفرار منه على الاستحباب والاحتياط لا للوجوب)
Wannan shi ne kusan duka abin da malaman Musulunci suka tafi a kai, don karin bayani duba (Hashiyat al-Adawi 2/ 491).

AKAN ABUBUWAN DA SUKA GABATA NA NASSOSHI, AKWAI ABUBUWAN LURA, DAGA CIKINSU:
1- Akwai bambamci tsakanin hukuncin yin jam’i ga mutum daya ko wasu mutane a wani yanki na gari, da kuma hukuncin al’umar gari gaba daya su dakatar da sallar jam’i a masallatai; Na farkon (sallar jam'i kan daidaiku) akwai sabanin malamai kan wajibcinsa, amma na biyun (al'uma gaba daya su bar jam'i) ijma’in malamai ne babu sabani a kan wajibcinsa. 

Don Haka:
I. Yin fatawa a kan kulle masallatai na gari gaba daya warware ijma’i ne, ma’ana; malaman Musuluncin gaba daya sun hadu a kan hakan cewa; sarayar da salla a gari gaba daya bai halatta ba. 
II. Fatawar malamai a kan sallar jam’i ba wajibi ba ce, wannan haka yake a kan mutun daya ko wani bangare na mutanen gari, amma ba shi ba ne hukucin sallar jam’i na gari gaba daya, domin ita wajiba ce kuma ba ta da makwafi (babu wani abu mai maye gurbinta), dole ne a samu wasu masallatai su yi sallar jam’i Ibn AbdulBarr yana cewa: (An yi ijma'i kan cewa ba ya halatta mutune su hadu a kan dakatar da masallatai, Idan an yi sallar jam’i a wani masallacin to sallar mutun daya a gida ta yi).
(لِإِجْمَاعِهِمْ عَلَى أَنَّهُ لَا يَجُوزُ أَنْ يُجْتَمَعَ عَلَى تَعْطِيلِ الْمَسَاجِدِ كُلِّهَا مِنَ الْجَمَاعَاتِ، فَإِذَا قَامَتِ الْجَمَاعَةُ فِي الْمَسْجِدِ فَصَلَاةُ الْمُنْفَرِدِ فِي بَيْتِهِ جَائِزَةٌ)
III. Yin sallar mutun daya ko wasu bangare na mutane a masallaci yana da makwafi babu shakka, amma samar da sallar jam’i a wasu masallatai lalurace ba ta da makwafi, domin wajibi ne da za a iya sauke shi. Annabi SAW ya ce: Babu wasu mutum uku a gari ko a kauye da ba sa yin sallar jam’i face sai Shaidan ya gallabe su. (Abu Dawud hadisi 547).
2- Ba a rawaito rufe masallatai ko dakatar da jam’in gaba daya gari ba a zamanin Annabi SAW da sahabbai; ko a Madinah a zamanin Annabi da zamanin Sayyidina Umar, ko masallatan kasar Shaam a shekara ta 18, ko masallacin garin Basrah a shekara ta 65, (duka wadannan sun faru ne a zamanin sahabbai).
3- Idan an kaddara cewa su sahabban sun dakatar da sallar jam’i da masallatai a kasar shaam, toh a wani lokaci hakan ya faru? sai da aka mutu, mutuwa mai yawa, kuma abin ya ki tsayawa? Ko tun farkon tsammanin cuta? kenan babu hujja a cikin wannan tarihi na sahabbai ga wadanda suka dakatar da sallah a gari gaba daya kafin bayyanar cuta ko tsananin mutuwa.
4- Neman magani ko kaurace wa mai cuta ba wajibi ba ne, amma yin sallar jam’i a wani masallaci ko a wasu masallatai a gari wajibi ne, ke nan ba daidai ba ne mustahabbi ya hana wajibi matukar akwai yadda za a yi wannan wajibin ya samu, kuma ke nan babu cin karo ballantana a ce za a ajiye hakkin Allah.
5- Da matukar wahala a ce annobar da ta kashe mutum sama da dubu dari biyu (200,000) a kwana uku a ce wai ba ta da saurin yaduwa, ballantana a ce ita cutar Corona tana da saurin yaduwar da ba a sami irinta ba a tarihi, ko a ce tafi annobar da ta faru a Madinah, duba yadda aka siffanta ta (موتا ذريعا) wato: mai saurin kashe mutane barkatai da yaduwa da yawa.
6- Saurin yaduwar annoba ta hanyar cakuduwa da juna, da yawan mutuwa a sakamakonta ba sabon abu ba ne, kenan ya kamata duk hukuncin da za’a fitar na Shari’a ya zamto ba sabo ba ne, ma’ana; kamata ya yi a samo shi daga Manzon Allah SAW kaitsaye ko magabatan farko.
7- Ashe zai iya yiwuwa a kamu da annoba ana cikin gida ta hanyar kofi ko kwano, ko a gidan abinci (restaurant) ko cikin ruwan da kamfanin ya kera, idan aka yi sakaci, idan har annobar irin wadda Allah ke sakko da ita ce.
8- Idan har za a iya sallar jam’i ko da mutum biyu ne (liman da ladan) a cikin masallaci, toh bai halatta a yi watsi da wannan damar ba, da ko wacce irin hujja. haka kuma, za a iya sauke wajibcin sallar Juma’a ko da da mutum 13 ne tare da liman, saboda Ka’idar da aka yi ishara a baya cewa; abin da zai yiwu ba a sarayar da shi (الميسور لا يسقط بالمعسور), kuma idan mutane suka yi watsi da wannan ikon sun yi laifi gaba dayansu.
9- Idan akwai inda ya kamata a dakatar da sallar jam’i saboda uzurin mutuwa to lallai a Salatul Khaufi ya fi kamata Annabi SAW ya yi hakan, kuma ko da hukuncin hakan bai zo ba a cikin Al-Kur’ani.
10- Kuma shin Annabi SAW bai lura da ka’idojin (mashaqqa da mas’laha) ba ne a sallar yaki? Ko kuma bai lura cewa sallar jam’i hakkin Allah ba ne? saboda haka dakatar da shi jam'in babu wata damuwa? Ko kuma lura da Maqasid (Manufofin Sharia) sai a dakatar da sallar jam’i a lokacin yaki, ko kuma su wadannan ka’idoji suna da wareren da a ke amfani da su a kebe?
11- An samu a Sharia inda aka yi rangwame a kan sallar jam’i saboda uzurin da bai kai mutuwa ba, kuma an samu makaho a zamanin Annabi SAW wanda bai da danjagora ya nemi uzuri a kan sallar jam’i kuma ba a bashi ba, kamar yadda aka samu an yi sallar jam’i a inda a ke ganin mutuwa kuru-kuru.
Kenan; hujjojin da ake kafawa kan dakatar da masallatan gari gaba daya da hujjar kare rai, ko da sunan saukin addini, suna da bukatan a kara nazari a kansu. 
12- Kamar yadda hadisi ya nuna; Idan Allah ya daura shedan akan al’umma sakamakon watsi da sallah a masallaci alhali suna da ikon samar da koda kadanne; to babu shakka, babu wani kasuwanci ko tsaro da zai inganta musu al’amuran rayuwansu.

BABBAN ABIN TAMBAYA AKAN DUK JAWABAN DA SU KA GABATA:
Shin zai iya yiwuwa a sauke wannan wajibi da ya tabbata ta hanyar aikin Annabi SAW da kuma ijma’in malamai a wannan yanayi na wannan cuta? 

Amsa:
1. A lamarin sallah, hukuncin jam’i na farawa ne daga mutum biyu, mai zai hana a ce liman da ladan ko mutun 3, su gabatar salloli a cikin masallatai? Kada a saba wa Allah gaba daya?.
2. Sallar Juma’a a mazahabar Malikiya ana iya yin ta da mutum 12 ko 13 da liman, mai zai hana yan kwamitin masallaci da su da liman su gudanar da sallar Juma’a, a rufe masallaci, sauran mutane su hakura.
3. Mai zai hana in hakan bai samu ba, a zabi wasu masallatai a cikin kowacce jaha wadanda za su cigaba da sallah kamar yadda a ka yi a Makkah da Madinah?
4. Mai zai hana in abin ya yi wahala, a zabi wasu salloli a rinka yin su a masallaci, lamarin da za a iya sa ido kada mutane su wuce adadin da ake so. 
5. Mai zai hana a dauki matakan da ake dauka a sauran wurare a masallatai?
 Idan aka ce mutane ba za su yi biyayya a kan hakan ba, hakan ba zai hana a sanya dokar ba, saboda babu wata doka a duniya da mutane ba sa karya ta, kuma hakan bai hana sanya ta ba ko fadinta, kuma ko a kan Korona da takaita zirga-zirga doka nawa ne mutane suka bi su dari bisa dari? 
 Kuma shin tunanin ake cewa mutane ba za su yi biyayya ba yana hana bayyana hukuncin Allah da yin bayaninsa? Musamman abin da ya tabbata cewa wajibi ne a kan daukacin al’uma?

TABBAS A GANINA YA KAMATA KOWA YA GAMSU DA ABUBUWA KAMAR HAKA;
1- Lallai wannan cuta jarabawa ce, amma tattauna hukuncin masallatai da salla ba ya nuna wasa da ita ko rashin gamsuwa da hadarinta.
2- Tattauna hukucin shari’a bai nuna kira zuwa ga bore, ko fito-na-fito ga dokokin da hukumomi suka dauka.
3- Dukkan matakan da ake dauka; tun daga addu’a har kasa, sabubba ne na kariya, babu wanda yake yakini ne kan hana yaduwar cuta, saboda hakikanin mai tsarewa shine Allah.
4- Dakatar da wanda aka tabbatar yana da cuta ko wani abu da zai takura wa masallata a masallaci abu ne da Annabi SAW ya yi a lokuta mabanbanta, kuma babu sabani a kan halaccin haka.
5- Shawarwarin likitoci kan matakan kariya ba sa rufe kofar yin bincike a kan hukuncin Sharia a kan wani abu. 
6- Hukuncin da wata kasa ta yi a kan wani abu na Sharia, ba ya zama hujja da ya wajaba kowane Musulmi ya bi.
7- Natsatsiyar tattaunawa kan hukunce-hukuncen Sharia ba ta kawo hatsaniya a cikin al’uma. 

TAMBAYOYIN KAMMALAWA DOMIN YIN NAZARI:
Idan da za a kaddara tabbatar Corona Virus tsawon rayuwar mutane, ko zuwan wata cutar daban (Allah Ya tsare);
- shin za a cigaba da kafa dalilan da a ke kafawa a yanzu, sai a kara rufe masallatai tsawon rayuwa?
- Idan ba za a yi hakan ba, to da wani dalilin? 
- Mai zai hana a yi anfani da dalilan a yanzu? 
- Ko akwai bambamci ne wurin halaccin rufe masallatai tsawon wata daya, da kuma rufe su tsawon wata 100, ko tsawon rayuwa?

Godiya ta tabbata ga Allah SAW.
Post a Comment (0)