*SIRRIN MALLAKAN MIJINKI*
*_Yadda Ya Kamata Dakin Ma'aurta Ya Kasance A Lokacin Saduwa_*
Ya kamata dakin ma'aurata ya kasance kamar haka; A duk yayin da suka nufi saduwa da junansu a cikin dare ne ko rana. Kamar yadda sunnar Manzon Allah ta tsara kamar haka;
1. Dakin ya kasance babu wani mutum a cikin ko da yaro ne.
2. Daki ya kasance a lokacin mai nutsuwa.
3. A samu karancin mutane a kusa da wajen.
4. Dakin ya kasance a kulle yake.
5. Sannan a kashe fitilar cikin dakin.
6. Abin kwanciyar ya kasance ba mai motsi ba.
7. Dakin da abin kwanciyar su kasance mafi dadin kamshi.
8. Ma'aurata su kwanta a tube ba tare da tufafi ba, amma ba laifi ba ne in sun kwanta da kaya a jikinsu.
9. Su kwanta a cikin mayafi guda daya, amma ba laifi ba ne in sun kwanta a mayafi daban-daban.
10. Su ambaci sunan Allah kafin su fara saduwa.
11. Daki ya kasance ba hayaniya.
Wabillahi Taufiq.
Rubutawa: *Abu Imam (Auwal Abdullahi)*
Gabatarwa: *Abu Imam (Auwal Abdullahi)*
*- Zauren Macen Kwarai-*
*. Ga masu buqatar shiga Zauren Macen Kwarai sai a turo da cikakkiyar sallam tare da cikakken suna da Address ta wannan Number +2348036692586,08062828025 a WhatsApp.*