TAMBAYA TA 145


TAMBAYA 1,724
Assalamu alaikum, Malam idda Wata nawa ne mace takeyi tagama?
AMSA
Idda shine lokaci da Allah ya ɗebawa mace ta jirashi kamin yin aure bayan rabuwa da mijinta, ko mutuwarsa sannan Allah ya ɗaurawa mace idda ne saboda dalili kamar haka:
1. Kuɓutar da mahaifarta saboda kada ruwan maniyyi maza sama da biyu su haɗu akan yaro ɗaya
2. Domin nuna darajar aure
3. A baiwa mijin da yayi saki lokaci mai yuwa ya gane amfanin matarsa ko kuskurensa ko ita sannan idan sunyi nadama su nemi su koma
4. Bin dokar Allah kan bayinsa, saboda mace ta zauna wajen sauƙe haƙƙin mijinta da Allah yayi mata umarni daidai yake da Allah tayi wa biyayya
*NOU'O'IN IDDA*
1. sakakkiyar da mijin ya tara da ita wannan iddanta jini uku ne saboda faɗin Allah cikin suratul baƙara aya ta 228 ((sakakkun mata zasu zauna ga kawunansu jini uku))
2. Sakakkiyar da bata idda saboda ƙarancin shekaru ko tsufa wannan kuma iddanta wata uku ne saboda faɗin Allah cikin suratul Ɗalaƙ aya ta 4 ((wanda suke ɗebe tsammani daga al'ada cikin matanku idan kun yi shakka to iddansu wata uku ne da kuma wanda basa al'ada))
3. sakakkiyar da mijin bai tara da ita ba wannan babu idda akanta saboda faɗin Allah cikin suratul Ahzab aya ta 49 ((ya ku waɗanda kukayi imani idan kuka auri mata muminai sannan kuka sakesu kamin ku tara dasu babu wata idda da kuke dashi akansu))
4. sakakkiya mai ciki wannan iddanta ta haifar da abinda ke cikinta ne saboda faɗin Allah cikin suratul ɗalaq aya ta 4 ((da ma'abota ciki ajalinsu shine su haifar da cikinsu))
5. Wanda al'adarta ta ɗauke saboda wani sababi (kamar wanda tayi planning) wannan idan har jinin bai zo zata yi zaman wata tara sannan tayi idda na wata uku kenan iddanta ya zama shekara saboda abin da imamul shafi'i ya rawaito a cikin musnad juz'i na 2 shafi na 107 daga umar ɗan khaɗɗab (ra) cewa ((zata zauna wata tara idan har ciki bai bayyana ba sai tayi idda da wata uku ya zama shekara kenan)) sannan malamai sukace ita macen da tayi family planning ana la'akari da jininta ne idan akwai da kuma babu, don haka duk lokacin da jini ya zo ya ɗauke to tayi ɗaya idan ya sake dawowa to tayi biyu haka na uku, ko min kusancin lokaci tsakaninsu da kuma nisansjk shi yasa tana iya gama idda da wuri kuma tana iya yin jinkiri
Wannan bayanai na cikin:
Fiqhussunah linnisa na Abu malik shafi na 565-566, Almugni na ibn ƙudama juz'i na 7 shafi na 466, alfiqhul islami wa adillatuhu juz'i na 7 shafi 625, i'ilamul muwaqqi'in na ibnul qayyim juz'i na 2 shafi 85, sharhin muwaɗɗa Na uthaimin juz'i na 2
Wallahu aalam
Amsawa: Mal Adam Daiyib
Post a Comment (0)