KIYAYE ABINDA YAKE DAIDAI SHI NE MAFI WAHALA A WANNAN ZAMANI


*KIYAYE ABIN DA YAKE DAIDAI SHINE MAFI WAHALA A WANNAN ZAMANI!*


Abu ne mai sauki mutum ya ya ɓata dare baki ɗaya yana kallo da chartings da downloadings da sauraron waƙoƙi. Amma abu ne ami wahala a gare shi ya ya tashi yayi sallar tahajjud a daya biya ukun dare, balle yaje sallar asuba.

Abu ne mai sauki a wajen 'yan matan yanzu da burgewa su saka kaya matsattsu da fidda tsiraicinsu da shapes din jikinsu. Amma abu ne mai matukar wahala a wajensu su saka hijjabi da niqabi su rufe jikinsu da kyau.

Abu ne mai sauki a wannan zamanin Æ™awata alfasha da yi mata kwaskwarima da daukanta wayewa da burgewa wajen yadawa acikin mutane da kuma koya musu ita, ta hanyar mace ta dinga rawa a gaban mijinta ko suna rungumar juna da sunan wai soyayya, amma abune mai wahala a wajen irin wannan mutanen yin Umarni da kyakkyawa ta hanyar da ya dace da koyarwar addinin islama! 

Abu ne mai sauki yanzu ayi gulma a ci naman wani wanda yayi daidai ko akasin haka. Amma abu ne mai wahala wajen kare da tsare mutuncin wannan mutum da yayi maka ba daidai ba.

Abu ne mai sauki sosai wajen yi ma mutane hukunci (hisabi) da zarginsu da cutar dasu. Amma fa abu ne mai wahala ga mutanen da suke haka su zauna suyi nazari akan kansu su gano laifukansu da kurakuransu da yiwa kansu hisabi.

Abu ne mai sauki yin budurwa da zuwa wajenta kai tsaye da bata soyayyarka kamar matsoraci. Amma abu ne mai wahala kaje wajen mahaifinta ka tambaye shi aurenta ka mayar da ita matarka kamar namiji!
 
Abu ne mai sauki kallon wadanda ba muharramanka ba da kiransu da 'yan matanka ko kunya. Amma abu ne mai wahala wajen rintse idanuwanka da tsare kanka daga fadawa fitina.

*Kai abu ne mai sauki da burgewa wajen aikata abin da yake ba daidai ba amma abu ne mai wahala da ban mamaki wajen aikata abin da yake dai dai.*


*_Allah Ya Bamu Ikon Kiyaye Abin Da Yake Daidai Da Barin Abin Da Yake Sabaninsa Ne!_*


✍️Rubutawa: *Abdullah A Abdullah Abou Khadeejat Assalafeey* 🕊️💞
16/08/2019.


https://t.me/sawtulhikma

https://www.facebook.com/sawtulhikmah

_*🎙ZAUREN SAWTUL HIKMAH 🎙* (da'awar sunnah a social Media's) 🌎_

*• Ga masu buqatar shiga Zauren Sawtul hikmah sai a turo da cikakkiyar sallama tare da Cikakken suna da Address ta wadannan Numbobi kamar haka:- +2348060027244 ko +2348039375380 a whatsapp.*
Post a Comment (0)