*SIRRIN MALLAKAN MIJINKI*
*_Aure:_*
Ma’anarsa
A larabce ana ambatar kalmar da furucin *NIKAH* ko *ZAWAAJ*. Nikah na nufin shigar wani abu cikin wani abu. Kasancewar ma’aurata kan shiga junansu ya sanya larabawa su ka ari Kalmar bisa ma’anar aure. Zawaj kuma na nufin tagwaitakar dangi a bisa sabanin jinsi.
Misalin mace da namiji dukaninsu daga dangi guda suke, ma’ana dangin bani Adam a bisa sassabawar jinsi. Namiji ya fito daga jinsin mazaje ma’abuta mazakuta yayinda mace ta fito daga jinsin mata ma’abuta matunci.
Amma Kalmar aure a shar’ance tana nufin wata mu’amular zamantakewar mace da namiji bisa amincewar junansu a kan sharudan da shari’a ta gindaya. Sunnar halitta ce dauwamammiya domin wanzar da irin dan Adam a doron kasa ta hanyar yawaitarsu don dorewar rayuwa. Haka lamarin yake ga dukkan sauran ababan rayuwa cewar Allah ya halicci dukkan halittu bisa zubin mace ne da namiji, cikin littafinsa mai tsarki inda yake cewa: “Mun halicci kowane abu jinsi biyu (mace da namiji)” Suratul Zariyaat: 49
Zamantakewar namiji tare da mace sunnar Allah ce cikin halitar bani Adama da ya kimsa ma sa tun asalin zubin halittarsa da ya yi.
Wannan ya sanya haduwar mace da namiji zama wuri guda ta zama larurar rayuwa domin bukatuwarsu da juna, bukatuwar dabi’a farko sannan bukatar addini ko al’ada. Ba ma ga ‘ya’yan Adama ba, mu na iya ganin wannan Sunnah ta Jallah, gwani, mahalicci mai baiwa cikin dukannin halittunsa. Idan mu ka kawar da nazarinmu ga duniyar dabbobi zamu ga makamancin haka a duniyar tsirai da bishiyoyi hakanan ma sauran kwayoyin halittu wadanda idaniya kan gaza ganinsu ba tare da wani tallafin na’ura ba. Misali, a dabinai akwai maza da mata. Macen dabino ita ke ‘ya’ya.
Amma ‘yayanta ba su moruwa sai an kada mata kilili wanda shi kuma daga jikin namijin a kan yanke shi, kamar dai yadda a kan samu barbara a duniyar dabbobi.
Hakanan zamu iya ganin wannan tagwaitakar halitta a kwayar halittar iskar odygen, atom, da dai sauransu.
Tarihi Ma’anar tarihi a nan ba ya nufin lokacin da aka fara aiwatar da al’ada ko sunnar aure, domin mun fadi a sama cewa sunnar halitta ce wacce dan Adam ya tashi ne ya sami kansa cikinta.
Muna iya tunawa cewa mutune na farko Adam da Hauwa’u cikin wannan sunna a ka halicce su, don haka ya zama tafarkin rayuwar ‘ya’yansu. Wannan ya sa dole ne dan Adam ya rayu rayuwar aure imma dai aure na shari’ah ko akasinsa.
Tun da mun sani cewa bukatar mace ga namiji ko namiji ga mace bukata ce ta dabi’a kamar dai yadda ka kan nemi ruwa idan kishirwa ta kama ka/ki. Abinda yakamata mu bi diddigin tarihi shine yadda ake kulla dangantakar aure gabannin musulumci.
Aure a jahiliyar Larabawa.
Gabannin musulumci alakar aure na kulluwa ne ta wa]annan hanyoyi kamar haka:
1. Suna yin aure kamar yadda musulumci ya tanadar, ta hanyar neman mace a hannun waliyanta, sannan ya biya sadakinta tare da daurawar aure gami da shaidu. Wannan na daga ciki ragowar tafarkin addinin Annabi Isma’ila kasancewar jinsin Larabawan kuraisahawa ‘ya’yan Ismaila ne AS.
2. Sannan akwai Auren aro: Wannan aure kan kasance ne a inda wani ke sha’awar kirar halittar wani. Domin kwadayin ya sami irin jinsin kirarsa cikin zuriyarsa sai ya kan ara matarsa ga wannan da yake neman iri ta zauna da shi tsawon wani lokaci har dai ciki ya baiyyana sannan alakar ta yanke ta dawo gida
3. Akwai kuma Auren tarayya: Wannan aure, shine samuwar wasu mutane kamar tara ko goma su amince a kan mu’amala da wata mace daya. Idan ta sami ciki kuma ta haifu takan tara su gaba dayansu sannan ta jingina dan da ta haifa ga wanda ta ga dama cikinsu, shikenan daga wannan rana ya zama shine uban wannan jariri ko jaririyar ko da kuwa ba shine ubansa na asali ba.
4. Sannan akwai daya nau’in auren tarayya wanda ita macen ce ki yinsa. Ma’ana mace kan kulla mu’amala da mazaje sama da biyar bakwai takwas ko ma goma, kuma kowannensu ya na sane da juna. Idan ta haifu, ta kan kira masanin nasaba (k’afa) ya duba hallitar jaririn tare da yin nazarin kamannin mazajen domin ya fitar da ko wanene uban wannan yaron. Wanda duk ya nuna shine uban wannan da na ta, babu kuma mai yin jayayya cikin ragowar mazajen, shi kuma wanda a ka ba shi dan ba shi da ikon musantawa ko ki.
1. Gado: Sannan a kan sami aure ta hanyar gado. Ma’ana idan uba ko wani makusanci ya rasu ya bar mata, a kan raba matan ne cikin kayan gadon mamacin, ita kuma matar ba ta da ikon kin yarda da wanda ta fada cikin rabon gadonsa. Allah ya yi ishara da irin wannan aure cikin suratul Nisa’i inda ya yi hani da yinsa a aya ta 19 inda yake cewa: “Ka da ku mallaki mata (a matsayin kayan gado) bisa tursasawa”
Ko a nan yankin mu na Africa a kwai kabilun da suke da irin wannan nau’in mu’amalar aure. Zuwan musulumci ya rushe dukkan ire iren wadannan aure na jahiliyya ban da nau’in farko wanda ya yi muwafika da shari’ar Allah SWT.
Addinin musulumci ya kwadaitarwa al’umma yin aure ta hanyoyi da dama, kamar haka:
2. Ibada ne: Alkur’ani ya kwadaitar da musulmi yin aure ta hanyar ajiye shi a gurbin ibada. Ya nuna cewa sunna ce ta Annabawa magabata kamar yadda ya zo cikin suratul Ra’ad: 38 “Hakika Mun Aiko Da Manzanni Gabanninku, Dukaninsu Mun Sanya Su Magidanta” (masu iyali da ‘ya’yaye)
Cikin wani Hadisi kuma Manzo SAW na cewa “Abubuwa hudu na daga cikin sunnar annabawa, sune: kunya, turare, aswaki da kuma aure.
1. Arzikin ‘ya’ya da yalwar rayuwa: wani lokaci kwadaitarwar kan zo ta nunin cewa shine tafarkin cika burin samun ‘ya’ya da Karin albarkar rayuwa. Misali aya ta 22 cikin suratul Rum Allah SWT na cewa:
“Yana daga cikin ayyoyinsa (Allah SWT) halitta muku mataye(mazaje) daga cikinku (jinsinku) domin ku samu nutsuwa, sannan ya sanya tausayawa da jin kai a tsakaninku”
Hakanan yana cewa a suratul Nahl aya ta 72 “Allah SWT ya sanya mataye gareku, sannan ya baku (haifuwar) ‘ya’yaye da jikoki daga mataikunku, ya arzurtaku daga (ababa) tsarkaka”
Haka nan Hadisin Abu Huraira cikin littafin Tirmizi yana cewa Manzo SAW na cewa: Mutane uku Allah yace Hakki ne a gareshi da ya tallafa musu, sune: wanda ya fita gwagwarmayar daukaka addinin Allah, da bawan da a ka rubuta masa fansa yake kokarin biya, da kuma wanda ya yi aure domin kare kansa daga fadawa alfasha.
A Hadisin Anas cikin ruwayar Tabraniy da Hakim na cewa, Manzo SAW yace “wanda Allah ya arzurta shi da auren mace saliha, ya taimake shi da rabin addininsa, ya yi kokari ya ji tsoron ubangijinsa cikin ragowar rabin da ya rage ma sa.
Wabillahi Taufiq.
Rubutawa: *Abu Imam (Auwal Abdullahi)*
Gabatarwa: *Abu Imam (Auwal Abdullahi)*
*- Zauren Macen Kwarai-*
*. Ga masu buqatar shiga Zauren Macen Kwarai sai a turo da cikakkiyar sallam tare da cikakken suna da Address ta wannan Number +2348036692586,08062828025 a WhatsApp.**SIRRIN MALLAKAN MIJINKI*
*_Menene So?_*
Shi dai so ya kasu kashi-kashi a takaice, shi ne zuciya ta ji tana son wani abu, hakan na iya faruwa ta hanyar jin jin labarin mutum, sauraron muryarsa ko kuma ganinsa a zahiri. A irin wannan yanayi dan’adam yake tsintar kansa da shaukin son kasancewa tare da abin da ya kamu da sonsa.
Allah (SWT) shi ke da ikon sanyawa dan’adam soyayya wani a zuicya, shi ya sa wasu lokuta da dama, idan aka kamu da so ba a iya rabuwa, domin ba yin mutum ba ne, yin Allah ne.
Soyayya Shi ma ya kasu kashi-kashi sai dai in yi bayani a takaice tun da na gaban zamu rika tattaunawa a kai.
A wata ma’anar, Soyayya na nufin isar, watau yin sa a aikace musamman idan wanda ake so ya amince. Da zarar haka ta faru, shi ke an wannan So din ya koma soyayya. Ba a yin soyayya dole sai zukata biyu sun aminta juna, idan ta kasance bangare daya ne kawai yake fama da so, dan’uwansa bai damu ba, to wannan ba soyayya ba ce.
Soyayya ba ta cika dole sai bangarori biyu sun damu da juna, ta hanyar kyautatawa, kulawa da kuma begen ganin juna ko jin muryoyin juna.
Shakuwa
Shakuwa na da dangantaka ko na ce alaka da soyayya, domin duk wanda ya ce soyayya dole a samu *SHAKUWA* a cikinta. Ba lallai ne duk wanda ya shaku da wani to dole sai sun yi soyayya ba.
Sai dai wata shakuwar takan koma soyayya dalilin kulawa da juna tsakanin saurayi da budurwa.
Amma soyayya sam ba ta yiwuwa matuka babu shakuwa, domin ita tamkar wani sinadari ne yake kai zuciyoyi dausayin da za su fara tunanin ba za su iya rayuwa ba tare da juna ba.
A takaice, Shakuwa tana nufin kasancewa tare da abinda ake so na tsawon lokaci ba tare da an gundiri juna ba.
Wabillahi Taufiq.
Rubutawa: *Abu Imam (Auwal Abdullahi)*
Gabatarwa: *Abu Imam (Auwal Abdullahi)*
*- Zauren Macen Kwarai-*
*. Ga masu buqatar shiga Zauren Macen Kwarai sai a turo da cikakkiyar sallam tare da cikakken suna da Address ta wannan Number +2348036692586,08062828025 a WhatsApp.*