DANCING FOR NY HUSBAND 1

*DANCING FOR MY HUSBAND*


RUBUTU NA 0️⃣1️⃣


_✍️Wannan itace sabuwar shegantakar da shigo cikin wannan al'ummar ta musulmi_

إنا لله وإنا إليه راجعون!!!😔


Yan uwana Musulmai, idan muka kalli irin rayuwar da muke yi a yanzu zamu ga ta sha bambam da ta baya saboda fitintinu sun mana yawa, mune cikin yawan yaƙe-yaƙe, kashe-kashe, tsanantawa a wajen rayuwa, da kuma rashin adalci na shuwagabanni, tsadar rayuwa, tashe tashe hankula, kidnapping, fashi, sata, rashin albarka acikin rayuwa da makamantansu wanda hakan yay ta haifar da tambayoyi da yawa daga wajen mutane kan cewa: *_Mai Ya Kawo Wannan Musifun? Musamman mu anan arewacin Nigeria!?_*

*Mai muka yi muka cancanci wannan? Ina muka dosa ne acikin rayuwar nan? Kuma mene ne za mu yi don hana faruwar wannan alamura?*

Yayin da masu hankalin cikinmu suka zurfafa tunani da tantance abinda ya haufar mana da wadannan fituntinu se suke kokarin gano amsar wadannan tambayoyi.👇


shin muna yin rayuwarmu ne ta fuskar bin maganar Allah - (Alqur’ani) - da kuma abin umarnin manzonsa (ﷺ) ko kuwa!?

 Amsoshin tambayoyin a bayyane suke cewa: *Mafi Yawanmu muna rayuwa ne a yanzu ta hanyar sanya Alkurani da Sunnar Manzon Allah (ﷺ) a gefe guda. Mun bar Alqurani har ya fara ƙura, na cikin wayar mu da na'urar mu kuma har sun gaji suyi deleting din kansu ma. Sunnar Manzon Allah kallonta muke wata abace wacce bin ta sai yan kauye da wanda basu waye ba, don har kunya muke ji wajen nunata a cikin halayenmu da rayuwarmu ma baki daya!*


Sai gashi kullum wasu fitintinun ne suke kuma bullowa wanda kwanan nan akayi ta yaki da masu *_Pre Weeding Pictures_* sai gashi wata sabuwa ta fito kuma mafi muni da batanci wanda ana neman tsokano Allah ne *_matan aure da mazajensu suna rawa wasu ma da iyalansu suna video suna dorawa duniya ta gani, wasu ma tsirara suke da kayan bacci, wasu suna rungume juna, wasu ma lalacin abin acikin dakin bacci akan gadonsu_* إنا لله وإنا إليه راجعون 🤦‍♂️ Malam Ina Muke Son Zuwa Ne? 

Irin wannan rayuwar da muke yi ko dabbobi basa yi wallahi, to amma babban dalilin faruwar hakan shine Barin Allah da mukayi da kuma koyarwa ta Abul Qasim (ﷺ). Gami da rashin kunya da muka dorawa kanmu.daman Annabi S.A.W yace.

_*Idan banajin kunya ka aikata abinda kaso*_

 Babu ko shakka wannan abinda wasunmu ke aika tawa akwai rashin kunyarAllah da kuma bayinsa.



Shiyasa babban malamin nan masani *_Shamsudden Muhammad Abi Bakar Ibn Qayyim Jauziyyah_* yake cewa:

*_Duniya ta girgiza, Sammai sunyi duhu, musifa ta bayyana akan ƙasa da teku saboda muguntar mugaye, da masu aikata mugunta. Albarkatu sun shuɗe, kyawawan ayyuka sun ragu, rayuwa ta ƙazantu saboda muguntar azzalumai. Hasken safe da duhun dare suna zubar da hawaye, saboda munanan ayyukan da ake yi a doran ƙasa. Malaman marubuta daga cikin mala’iku da wasu daga cikinsu sun koka ga Ubangijinsu saboda yawan barna da girman zalunci da yayi yawa a ƙasa._*

Me yasa muka kai zuwa ga irin wannan yanayin?🤔 Ga abin da ya malam ya faɗa a gaba don bayyana wannan sabon abu:

*_Lokacin da aka watsar da Alƙur'ani mai girma, da Sunnah, saboda ana tsammanin basu isa ba ga rayuwar dan adam, kuma idan aka nemi ra'ayin mutane, misalai, hankali, da kalmomin (sauran waɗanda ake kira) malamai, an lalata halayen mutane, lalatattun mutane suka cika. Zuciyoyinsu sukayi duhu, fahimtarsu ta rikice, kuma hankalinsu ya dagula._*


Malam ya ambaci cewa mun kai wannan matsayin ne saboda abubuwa kamar haka:

•Hankali ya maye gurbin hikima.

•Batan sha'awace-sha'awace sun maye gurbin dalili.

•Neman bata ya maye gurbin jagora.

•Kuskure ya maye gurbin abu mai kyau.

•Jahilci ya maye gurbin ilimi.

•Munafunci ya maye gurbin ibada.

•Haram ta maye gurbin halal.

•Karya ta maye gurbin gaskiya.

•Kuma rashin adalci ya maye gurbin adalci.

*_Idan ka ga mafi girman irin wannan mugunta da zalunci na mutane, kuma an sanya takensu a inda rundunarsu ke mamayewa, hakika kasan ƙasa zata fi soyuwa fiye da saman ta a wajen mutane, ƙwanƙolin tsaunuka za su fi soyuwa akan tuddai, kuma rakiyar dabbobi za ta fi ta mutane._*

*_📓AL-FAWA’ID: – na ibn Al-Qayyim_*


 _Mu hadu a rubutu nagaba..._


✍️Rubutawa: *Abdullah A Abdullah Abou Khadeejat Assalafeey* 💞🕊️

📝Gyarawa/dubawa: *Ummul Banat*

5/10/1441.
28/05/2020.

https://www.sirassalafeey.wordpress.com


https://t.me/sawtulhikma

https://www.facebook.com/sawtulhikmah

_*🎙ZAUREN SAWTUL HIKMAH 🎙* (da'awar sunnah a social Media's) 🌎_

*• Ga masu buqatar shiga Zauren Sawtul hikmah sai a turo da cikakkiyar sallama tare da Cikakken suna da Address ta wadannan Numbobi kamar haka:- +2348060027244 ko +2348039375380 a whatsapp.*

Post a Comment (0)