DEEPIKA PADUKONE

DEEPIKA PADUKONE

Jinjina ga Deepika 'ya a wajen Padukone
Wace kyawunta ke wuta da kanta ta ƙone
Mutum ko da ma shi wanene
Ba shi da zarrar ƙin 'yar Padukone
Ga jarumarata Deepika me kyawun kunne
Sannu sannu Deepika 'yar Padukone.

Kin fi su kyau da kuɗi jarumar mata
Kin fi matsayi su ɗin duka 'yan mata
Kin fi su sa'a da ƙwarewa duka mata
Ke ce fitilarsu Deepika ƙawata
Ke ce kika hasken dukka duhun mata
Sannu Deepika tauraruwar mata.

Kin cinye Indiya kin lashe su gaba ɗaya,
Kin cinye birnin Sin duk ke ɗaya
Kin ci galabar zukatan Amurkawa baki ɗaya
Kin mallake zuciyar mutanen Nijeriya
Ke ce kika karɓe zukatan mutanen Somaliya
A taƙaice dai Deepika ta mamaye duniya.

Fatan alheri da ke da mai gidanki 
Da iyayenki har ma da ƙawayenki 
Cikinsu haɗa duka harda 'yan uwanki 
Ki tuna ciki duka har da abokanki 
Allah yasa watarana mu ga 'ya'yanki 
In muna da rai ma wataƙila da jikokinki. 

Ni ne Jamilu katibin nan na Kaduna 
Me rattabe babu dare ko kuma rana 
Ko da da iska ko ruwa ko zafin rana, 
Na yi miki baituka domin son raina 
Da ƙwarewa a batuna na cikin magana 
Gashi waƙa na rera ta cikin hikima. 

©️✍🏻
 Jamilu Abdurrahman 
    +2348185819176
Haimanraees@gmail.com 

Post a Comment (0)