Gizo da Botorami
Ga ta nan ga ta nan ku.
Ta zo mu ji ta.
Gizo ne da Botorami. Sai ran nan Botorami zai yi tafiya, sai ya ce, “To Gizo, tsaya - ga amfanin gonata nan, zan yi tafiya Æ™auye. Ga shin nan amana duk abin da ya yi ka kwashe mini ka kai mini gari”. Sai Gizo ya ce, To, “sai ka dawo”, daman da Botorami sai ya tafi sai ya ce, Shi ke nan, sai Gizo ya noma gonar sa amfanin gonar yayi kyau. Shi kuma Botorami hatsinsa bai yi kyau ba ya fara lalacewa. Sai Gizo ya yanke masa ya je ya ajiye. Wadanda suka danyi kyau ya saka su a saman damin marasa kyau kuma ya saka a kasa. Haka ya samu audugarsa ma duk bat yi ba, sai ya sa ta. Wacce ta isa ya yayyaÉ—a a sama ya É—aure. Gero haka, dawa haka, maiwa haka, duk dai. Shi ke nan sai ya kai rumbu sai ya ajiye. Gizo kuma nasa ya yi shar-shar, ya yi kore shar abin sha’awa. Sai ya kai rumbu sai ya ajiye. Sai ran nan Botorami ya dawo. Sai ya ce da Gizo. Au! Har ka gyara kayan amfanin gonar. Sai ya ce, eh. Sai ya ce, To shi ke nan. Sai Botorami sai ya je ya ga ta sama mai kyau. Sai ya ce, ìTo na ga amfanin gona, na gode, na gode, madalla, madalla. Sai ya ce, ìTo shi ke nan.Ãà Sai ran ran gidan Botorami zaÃa yi girki. Da ya je ya buÉ—e dawa sai ya ga duk ba ta yi ba, ta sama ce ta yi kyau. Ya buÉ—e gero haka, ya buÉ—e dawa haka, ya buÉ—e gyaÉ—a haka. Sai ran sa ya baci bai ji dadi ba.
Sai ya É—ebe mai kyan, marar kyan sai ya bar ta a rumbu sai ya bunka wa runbun wuta. Shi ke nan sai ya je ya fara kuka, ya ce, Lailaha illallahu, Gizo ba ka san abin da ya same ni ba.
Sai ya ce, Ban sani ba. Ya ce, To duk kayan nan nawa mai kyau duk sun ƙone, na yi gobara. Sai ya ce, To shi ke nan, Allah ya kiyaye, Allah ya tsayar nan. Da safiya ta yi sai ya ce, To, a je a duba amfanin daya kone. Sai ya ce, To shi ke nan. Dama kuma Botorami ya zuba kuɗi a cikin rumbun daya kone. A tona, sai kuɗi. A tona, sai kuɗi, a tona, sai kuɗi. Sai Gizo ma sai ya ce, To ni ma bara na ƙone nawa ko ni ma zan samu kuɗi. Duk sai ya ƙone nasa mai kyan, da ya ƙone nasa mai kyan, sai ya je ya sa wa Botorami kuka. Ya ce, Ni ma na yi irin taka. Sai Botorami ya ce, To Allah ya kiyaye. Ya ce, To sai a je a duba amfanin gona. Shi ke nan, aka je aka dudduba duk ba a samu kuɗi ba sai toka. Sai Gizo ya sa kuka.
Kurunkus kan dan bera