TSAFTAR JIKINKI


SIRRIN MALLAKAN MIJINKI

TSAFTAR JIKINKI

Ya kamata akalla mace ta yi wanka sau biyu a rana, ta sauya kaya sau biyu, kadaki ce zaki saka kaya har su kwana biyu a jikinki, ki kula da tsaftace bakinki, da akwai wasu wurare da suka kasance matattarar datti ne a jikin yan ya mace, kwauri, hammata,cibiya,kasar mama,(nono), tsakanin cinyoyi.

Don haka dole sai mace ta kula da tsaftace wadannan guraren, rashin kula da su yana haddasa warin jiki, yin askin gashin hammata da mara a duk bayan wani dan lokaci shi ne maganin warin.

Tsaftar yaranki, ki kula datsaftar jikinsu da ta kayansu, ki tabbatar kin yi musu wanka kafin babansu ya dawo, ki samu wankakku kaya ki saka musu, hakan zai sanya mijinki ya ji dadi a zuciyarshi, ke kuma ki kara samun matsayi a gurinsa.

Ta bangaren sanya kaya kuwa idan muka koma ta wannan bangaren akwai kalar kayan da ya kamata ta sanya daddare.

Saboda da rana akwai yawan zirga zirgar jama'a zaki iya amfani da kaya wadanda ba zasu nuna tsiraicinki ba sosai ba, amma da dare ya yi ana so ki sanya kaya wadanda suke masu bayyanar da surorin jikinki ne, domin kuwa kada ki dauki I zumbuleliyar riga mai kama da ta sanyi ki saka, ki ga ko idan har kika yi haka babu abin da zai hana idan maigida ya shigo ya kalle ki ya yi tsaki.

Saboada haka sai ki yi kokari ki zama mace ta gari wadda idan mijinta ya kalle ta sai ya ji ranshi ya yi masa fari, ko kuma idan yana cikin bacin rai da ya kalleki ya ji duj wani kunci da yake cikin ranshi an tafiyar masa dashi.

Wabillahi Taufiq.

Rubutawa: Abu Imam (Auwal Abdullahi)

Gabatarwa: Abu Imam (Auwal Abdullahi)


Zauren Macen Kwarai

Ga masu buqatar shiga Zauren Macen Kwarai sai a turo da cikakkiyar sallam tare da cikakken suna da Address ta wannan Number +2348036692586,08062828025 a WhatsApp.
Post a Comment (0)