FAHIMTAR MATUƘAR SHA'AWAR 'YA MACE


*SIRRIN MALLAKAN MIJINKI*

*_Fahimtar Matukan Sha’awar ’Ya Mace:_*

Wani abun da ke kawo matsala cikin ibadar auren ma’aurata shi ne karancin ilmin yanayin sha’awar juna. Kamar yadda halittar mace da namiji ta bambanta, to haka halayyarsu, hankalinsu da kuma sha’awarsu. Shi namiji Allah SWT Ya inganta ma’aikatar hankalinsa, Ya ba shi karfin basira da aiki da hankali sama da wanda Ya ba ‘ya mace, ita kuma ‘ya mace, Allah Ya inganta ma’aikatar hankalinta da shau’uka masu tsananin karfi da inaganci, sama da na da namiji.
In muka lura da irin yanayin zamantakewar dan Adam, sai mu ga kowannen mu an ba shi abu mafi cancanta da shi a halin zaman rayuwar duniya. Maza su ne masu rike gida da al’umma gaba daya, dole suna bukatar kaifin hankali da basira wajen zartar da ayyukansu. Ita kuma mace, in so da kauna da tausayi ba su cika zuciyarta ba, ya za a yi har ta iya yin hakurin daukar ciki, raino ta kuma yaye ‘ya’yanta har a samu cikar al’umma?
Yanayin halittarmu yanayin sha’awarmu; da namiji hankali ya fi karfi cikin ma’aikatar hankalinsa, sannan ga kasantuwar sha’awarsa mai tsanantuwa, sai ya kasance biyan bukatar sha’warsa, kodayaushe ita ya sa a gaba, kuma in ya kusanci matarsa, to ba wani abun da zai hana shi cimma biyan bukatarsa, sai dai in akwai wata matsala ta daban. Ita kuwa mace, shau’uka ne suka fi karfi cikin ma’aikatar hanakalinta; kuma kamar yadda muka san rashin tabbas din shau’ukan dan Adam, domin dai ba shaukin da ke tabbata a zuciya kodayaushe, komin karfinsa kuwa, to haka sha’awar ‘ya mace take, ta kan caccanza kodayaushe, ba lallai ba ne abin da ya motso da sha’awa yau ya zama kullum shi zai rika motso da sha’awa. Maigidan da ya fahimci wannan, yana kuma son ya jiyar da matarsa, to sai ya rika sa ido sosai a kan yanayin caccanzawar sha’awarta.

Shau’uka kala biyu ne: Farare da bakake, misali ga kadan daga cikin irin shau’ukan da kan taka rawa cikin sha’anin sha’awar ‘ya mace:
Farare shauki:
Farin ciki
Jin dadi
Natsuwa
Wadatar Zuci
So da kauna
Bakake:
Yawan damuwa
Bakin ciki
Jin Haushi
Fargaba
kiyayya
Huzni

To kafin uwargida ta ji motsuwar sha’awa ta kankama ko’ina a jikinta da ma’aikatar hankalinta, akwai bukatar kasancewar shau’ukan da ke kai kawo cikin zuciyarta a wannan lokacin, ya kasance farare ne suka fi bakaken yawa. A takaice dai matukan sha’awar ‘ya mace guda uku ne: jin dadin zuciya; wasannin ibadar aure da kuma natsuwar rai.

Wabillahi Taufiq.

Rubutawa: *Abu Imam (Auwal Abdullahi)*

Gabatarwa: *Abu Imam (Auwal Abdullahi)*

*- Zauren Macen Kwarai-*

*. Ga masu buqatar shiga Zauren Macen Kwarai sai a turo da cikakkiyar sallam tare da cikakken suna da Address ta wannan Number +2348036692586,08062828025 a WhatsApp.*
Post a Comment (0)