SHARHIN FIM ƊIN BLACK PANTHER


SHARHIN FIM ƊIN BLACK PANTHER 

Black Panther fim ɗin jarumta ne da aka fitar a shekara ta 2018 a ƙasar Amurka, kuma labarin ya samo asali ne daga Litattafan almara na Marvel Comics. Black Panther shi ne fim na goma sha takwas daga cikin jerangiyar fina-finan duniyar Marvel wato (MCU). 

An sanar da tabbacin yin fim ɗin Black Panther a watan Oktoba na2014, yayin da daga baya Chadwick Boseman ya fito da wannan matsayi a cikin shirin Captain America: Civil War. 
Black Panther shi ne fim na farko da kamfanin Marvel suka yi wanda mafi yawancin mutanen cikinsa baƙaƙen fata ne. An fara ɗaukar wannan shiri ne a tsakanin watan Janairu zuwa Afrilun shekara ta 2017 a EUE/Screen Gems Studios da ke Atlanta da kuma Busan, South Korea.

An saki shirin Black Panther a birnin Los Angeles a ranar 29 ga watan Janairu 2018, yayin da kuma aka sake shi a ko'ina cikin ƙasar Amurka a ranar 16 ga watan Fabrairu na wannan shekara a matsayin ɗaya daga cikin fage na uku daga cikin fagagen fina-finan kamfanin Marvel. Fim ɗin ya samu yabo sosai daga masu sharhi musamman ga mai bada umurni, 'yan wasan, kayan sawa, na'urorin da aka yi amfani da su da dai sauransu. Mutane da dama sun yarda cewa wannan shiri yana ɗaya daga cikin fina-finan kamfanin Marvel mafi kyau, har ma an sanar da cewa yana daga cikin fina-finai goma da suka fi kowanne kyau a duniya a cikin shekara ta 2018. Haka kuma fim ɗin ya kawo kuɗi sama da dala biliyan uku a harkar kasuwancinsa na duniya baki ɗaya tare da kafa tarihi iri daban-daban a box-office ciki kuwa har da zama da yayi fim ɗin da baƙar fata ya bada umurni da yafi kowanne kawo kuɗi a duniya. Haka kuma shirin ya zamo shi ne shi ne shiri na tara da yafi kowanne kawo kuɗi a duniya baki ɗaya, shiri na uku da yafi kowanne kawo kuɗi a Amurka da Canada, kuma shiri na biyu da yafi kowanne kawo kuɗi a 2018 gaba ɗaya. 

Shin ya samu lambobin yabo da kuma damar shiga gasanni da dama, cikinsu har da Best Picture, Best Costume Design, Best Original Score , da kuma Production Design. Black Panther shi ne fim ɗin jarumta na farko da ya fara samun shiga gurbin gasar Best Picture, kuma shi ne fim ɗin MCU na farko da ya fara lashe gasar Academy Award. 

MA'AIKATAN SHIRIN 

• Bada umurni - Ryan Coogler
• Ɗaukar nauyi - Kevin Feige
• Rubutawa da tsarawa - Ryan Coogler & Joe Robert Cole
• Asalin labari - daga Black Panther wanda Stan Lee da 
Jack Kirby suka rubuta 
• Sautin Shiri - Ludwig Göransson
• Horas da 'yan wasa - Rachel Morrison
• Tacewa - Michael P. Shawver & 
Debbie Berman
• Kamfanin da ya shirya - Marvel Studios
• kamfanin da ya yaɗa - Walt Disney Studios
Motion Pictures
• Ranar Fita - 29, January 2018 ( Dolby Theatre )
February 16, 2018 (United States)
• tsawon Shiri - mintuna 134 
• Ƙasa - United States
• Harshe - English
• Kasafi - $200 million 
• kasuwancin Box-office $1.347 billion

LABARIN SHIRIN 

Dubunnan shekaru da suka gabata, wasu ƙabilu guda biyar a yankin Afirka sun kasance suna yaƙar junansu akan wani dutse mai daraja da faɗo daga sama wanda yake ɗauke da sinadarin Vibranium. Ɗaya daga cikin mayaƙan sai ya sha wani tsuro mai siffar zuciya wanda Wannan sinadarin ƙarfe ya taɓa. Hakan ne yasa ya samu gagarumin ƙarfi, daga nan ne ya zama Black Panther na farko. Wannan jarumi ya haɗa kan dukkan sauran ƙabilun baki ɗaya inda suka kafa ƙasar Wakanda, amma ƙabilar Jabari sai suka yi tawaye suka koma rayuwa a cikin tsaunuka. Kwanci tashi sai mutanen Wakanda suka dinga amfani da sinadarin Vibranium wajen ƙere-ƙere na gaban kwatance, amma sai suka ɓoye kansu a matsayin ƙasa mai ƙaramin ƙarfi wacce yanzu take tasowa. 


 A shekara ta 1992, sarkin Wakanda na wancan lokacin wato sarki T'Chaka ya ziyarci ɗan uwansa me suna N'Jobu wanda yake yi musu leƙen asiri a Oakland, California. T'Chaka sai ya zargi N'Jobu da laifin yin harƙallar makamai da wani mai harkar makamai me suna Ulysses Klaue ta hanyar nuna masa yadda zai yi ya saci Vibranium daga Wakanda. Abokin harƙallar N'Jobu sai ya bayyana cewa sunan shi Zuri, kuma shima ɗan leƙen asirin Wakanda ne, kuma ya tabbatar wa da T'Chaka zargin da yake yi gaskiya ne. 

A yanzu kuma, bayan mutuwar sarki T'Chaka, ɗansa wato T'Challa sai ya dawo Wakanda domin ya hau karagar mulki. Shi da Okoye, wacce ita ce shugabar masu tsaron sarki da ake kira da Dora Milaje sai suka ɗauko tsohuwar budurwar T'Challa me suna Nakia daga wani aikin sirri da ta je yi a dajin sambisa. 

Da aka zo bikin naɗin sarautar, sai shugaban ƙabilar Jabari da ake kira da M'Baku ya ƙalubalanci T'Challa da su gwabza domin neman karagar. T'Challa yayi nasara akan M'Baku kuma ya shawarce shi da ya miƙa wuya a maimakon ya kashe shi. 

Sanda Klaue da abokin aikinsa Erik Stevens suka saci wani kayan tarihi da ya fito daga Wakanda a London, sai abokin T'Challa kuma saurayin Okoye wato W'Kabi ya roƙe shi da ya dawo da Klaue a raye. Daga nan sai T'Challa, Okoye, da Nakia suka tafi Busan , South Korea, domin a can ne Klaue ya shirya siyarwa da jami'in hukumar CIA Everett K. Ross wannan sinadari na Vibranium. Anan ne faɗa ya ɓarke har dai T'Challa ya kama Klaue, inda da ƙyar ya barshi a hannun Ross domin ya bincike shi. Klaue sai ya faɗa wa Ross cewa yadda ake tunanin Wakanda a duniya fa ba haka take ba. Ana cikin haka ne sai ga Erik ya zo tare da abokansa inda suka ƙwace Klaue yayin da shi kuma Ross ya samu mummunan rauni wajen taimakon Nakia. Maimakon ya bi Klaue, sai T'Challa ya ɗauki Ross ya tafi da shi Wakanda, domin a can suna da fasahar da za su iya ceto ransa da ita. 

Yayinda Shuri ke ƙoƙarin warkar da Ross, T'Challa sai ya tunkari Zuri dangane da N'Jobu. Zuri sai ya bayyana mishi cewa N'Jobu ya shirya raba raba kayan ƙere-ƙeren Wakanda ne tare da sauran baƙaƙen fata na duniya domin ya taimaka musu su yaƙi masu yaƙarsu. Yayin da sarki T'Chaka ya kama N'Jobu, sai ya yi yunƙurin hallaka Zuri wanda hakan yasa T'Chaka ya kashe shi. T'Chaka shi ne ya umurci Zuri da ya yi ƙaryar cewa N'Jobu ya ɓace, kuma ya bar ɗansa domin hakan shi zai tabbatar da ƙaryar. Wannan yaro shi ne ya girma ya zama Soja Stevens a ƙasar Amurka wanda ya ɗauki inkiyar "Killmonger" a matsayin sunansa. 

Ana cikin haka ne kuma, sai Killmonger ya kashe Klaue ya kuma tafi da gawarsa Wakanda. Bayan an kawo shi gaban tsofaffin birnin, sai ya bayyana asalinsa a matsayin N'Jadaka kuma ya buƙaci a bashi damar hawa karagar mulki. Daga nan sai Killmonger ya ƙalubalanci T'Challa da su yi faɗa domin a tantance. To a garin hakane ya kashe Zuri kuma yayi galaba akan T'Challa ya jefa shi cikin ruwa. Bayan Killmonger ya sha ɗan wannan tsiro, sai ya umurce su da su ƙona sauran gaba ɗaya, amma Nakia ta samu damar ɗaukar guda ɗaya kafin su ƙone. Killmonger, tare da goyon bayan W'Kabi tare da mayaƙansa sai suka shirya rarraba makamai zuwa sauran sassan duniya. 

Nakia, Shuri, Ramonda, da Ross sai suka gudu zuwa ga ƙabilar Jabari domin neman mafaka. A can ne suka iske T'Challa a sandare cikin dusar ƙanƙara, ashe sun tsinto shi ne daga ƙasan Kogin da ya faɗa shi ne suka cece shi domin su biya bashin halaccin da ya yi wa M'Baku's life. Bayan Nakia ta bashi wannan ɗan tsuro, sai T'Challa ya warke, kuma ƙarfinsa ya dawo. Don haka sai ya tunkari Killmonger wanda shi ma ya sanya tasa rigar ta Black Panther. W'Kabi tare da mayaƙansa sai suka fara yaƙar Shuri, Nakia, da kuma mayaƙan Dora Milaje, yayin shi kuma Ross ya ke ƙoƙarin kaɓo jiragen da ke ƙoƙarin fita da makaman. M'Baku da mayaƙan Jabari suma sai ga su sun kawo wa T'Challa ɗauki. Yayinda Okoye ta tunkari W'Kabi, sai shi da mayaƙansa suka miƙa wuya. Su kuma T'Challa da Killmonger a ɓangaren nasu faɗan, T'Challa ya samu damar caka masa wuƙa wanda hakan ya yi masa mummunan rauni. Duk da cewa T'Challa ya bashi shawarar ya miƙa wuya ya bari a warkar da shi, Killmonger sai ya ƙi amincewa tare da bayyana cewa ya yarda ya mutu a matsayin mutum mai 'yanci. 

Bayan mutuwarsa, sai T'Challa ya gina gidauniyar taimako a inda N'Jobu ya mutu tare da bayyana Nakia da Shuri a matsayin waɗanda za su tafiyar da wannan wuri. A ƙarshe dai an nuno T'Challa ya bayyana a taron majalisar ɗinkin duniya domin bayyanawa kowa asalin yadda Wakanda take. A wata nunowa ta ƙarshe kuma, an nuno Shuri tana taimakawa Bucky Barnes dangane da jinyar da yake yi. 

JARUMAN SHIRIN 

• Chadwick Boseman - T'Challa / Black Panther 
• Ashton Tyler - T'Challa yana ƙarami 
• Michael B. Jordan - N'Jadaka / Erik "Killmonger" 
• Seth Carr - Erik Yana ƙarami 
• Lupita Nyong'o - Nakia
• Danai Gurira - Okoye 
• Martin Freeman - Everett K. Ross
•Daniel Kaluuya - W'Kabi 
• Letitia Wright - Shuri
• Winston Duke - M'Baku
• Angela Bassett - Ramonda 
• Forest Whitaker - Zuri :
• Andy Serkis - Ulysses Klaue
• John Kani - T'Chaka 
• Florence Kasumba - Ayo 
• Sterling K. Brown - N'Jobu
• Isaach de Bankolé 
• Connie Chiume 
• Dorothy Steel 
• Danny Sapani 
• Sydelle Noel 
• Marija Abney,
• Janeshia Adams-Ginyard
• Maria Hippolyte
• Marie Mouroum
• Jénel Stevens
• Zola Williams
• Christine Hollingsworth
• Shaunette Renée Wilson 
• Sebastian Stan 

NASARORI DA GURBIN GASANNI DA SHIRIN YA SHIGA 

1. American Music Award (won)
 2. BET Awards (winning two)
 3. ONE Billboard Music Award
 4. ONE British Academy Film Award (won)
 5. TWELVE Critics' Choice Movie Awards (winning three)
 6. Golden Globe Awards
 7. EIGHT Grammy Awards (winning two)
 8. SEVEN MTV Movie & TV Awards (winning four)
 9. ONE MTV Video Music Award (won)
10. SIXTEEN NAACP Image Awards (winning ten)
11. FIVE People's Choice Awards (winning two)
12. FOURTEEN Saturn Awards (winning five)
13. TWO Screen Actors Guild Awards (winning both)
14. ELEVEN Teen Choice Awards (winning three)
15. Academy Award for Best Picture
16. Golden Globe Award for Best Motion Picture – Drama

Ana sa ran kashi na biyun wannan shiri zai fita a 2022
Post a Comment (0)