KATRINA KAIF


KATRINA KAIF

Katrina abar ƙauna
Katrina mai daɗin suna
Kyakkywa ce ita Katrina
Kallonki na sanyaya mini raina
Murmushinki na ƙawata raina
Ƙwarewarki ta shanye tunanina
Juriyarki ta haye hashena
Jajircewarki ta ruɗa mafarkaina
Kafiyarki ta sani cikin ƙauna
Wayyo Wayyo Katrina mai kyau abar ƙauna.

Wajen rawa Katrina tana burge kowa
Wajen iya soyayya tana nishaɗantar da kowa
Gashi ta ƙware a dambe da kokawa
Tana da masoya a cikin Indiyawa
Tana da masoya a cikin Larabawa
Tana da masoya a cikin Amurkawa
Tana da masoya a cikin Hausawa
Tana da masoya a cikin Japanawa
Tana da masoya a cikin farisawa
Katrina tana da masoya har ma cikin yarbawa.

Kallon idonta kan sani cikin shauƙi
Kalmanta na da zaƙi
Murmushinta kan sani shiga yanayi
Kai da ganin sifarta ka godewa buwayi 
Dariyarta kan sani jin nishaɗi
Muryarta a koyaushe tana da daɗi 
Wannan mace gaskiya ta ko'ina ta yi 
Duniya ta sanda ke ake yayi 
Maƙiyanki ko da gardama sun yi 
Da sun gane ki sai su koma wasu bayi. 

Ni ne Masoyinki Jamilu Abdurrahman 
Fatan ƙaunarki ko kaɗan za ki sammin 
Ko da ragowa ce na yarda abar min 
Don Allah murmushinki nake so ki ɗan min
Don Allah dariyar ki nake so ki ɗan min 
Don Allah tafiyarki nake so ki ɗan min 
Don Allah ɗan farin nan naki ki yi min 
Ko da murguɗa baki ne ma duk ki yi min 
Ko ma duka ne duka na yarda ki yi min 
Koma menene na yarda ki yi min. 

©️✍🏻
 Jamilu Abdurrahman 
    +2348185819176
Haimanraees@gmail.com  
 27 June 2020 
Post a Comment (0)