*_ANNABI S.A.W SHINE MAFI ALKHAIRIN MAI GIDA_*
Annabi s.a.w shine mafi alkhairi mutane baki daya,kuma shine mafi alkhairin mutane awajan iyalinsu,kamar yadda ya tabbatar da haka da harshensa mai albaka kuma ya tabbatar da hakan a aikace.
Annabi s.a.w yana cewa:
*(Mafi alkhairi kuma zabbe acikinku,shine mafi alkhairi kuma zabbe wajan iyalinsa,kuma nine mafi alkhairi kuma zabbe awajan ga iyalina)*.
@سنن التّرْمِذي.
Hakika Annabi s.a.w ya aikata hakan ga iyalinsa da yake tabbatar da shine mafi alkhairin mai gida acikin dukkan mutane baki daya.
Annabi s.a.w ya buya misali mai yawa cikin kyautata ma iyalinsa agurarw da dama ga kadan daga cikinsu.
●Annabi s.a.w ya kasance mai kyautata mu'amala da tausasama iyalinsa har ya kasance yana zama awajan rakuminsa ya durkusar da gwaiwarsa sai matarsa Safiyya ta dora kafafuwanta akan cinyoyinsa har sai ta hau kan rakuminsa.S.A.W
@صحيح البخاري
●Annabi s.a.w ya kasance yana kiran sunan matarsa Aisha, sai ya yanke sunan dan ya faranta mata rai sai yace:
*(YA A'ISH)*
@صحيح البخاري.
Wani lokacin ya kan kirata da:
(BINTIS SIDIQ)
@سنن الترمذي وسنن ابن ماجة
Dan Girmamata da girmama iyalin gidansu da nuna mata soyayya da kauna.
●Annabi s.a.w ya kasance yana yima iyalinsa hidima.
Daga Aswad bn Yazid R.A yana cewa:na tambayi nana Aisha R.A wani aiki Annabi s.a.w yake idan ya shiga gida?? Sai tace:
*"Ya kasance idan ya shiga gida yana cikin yin hidima ga iyalinsa idan an kira sallah sai yafita zuwa Sallah"*.
@رواه مسلم والترمذي.
Daga Anas dan Malik R.A Yana cewa:
Annabi s.a.w ya kasance awajan daya daga cikin matansa,sai daya daga cikinsu da aika masa da wani dan kwano da abinci mai dadi acikinsa, sai matar da Annabi s.a.w yake dakinta ta sanya hannunta ta bige kwanon abinci ya zube kuma kwanon ya fashe, sai Annabi s.a.w ya hada wannan fasheshshan kwanon ya zuba abincin acikinsa,yana cewa:
*(Mahaifiyarkuma haka tayi kishi) sannan ya zaunar da khadimin da ya kawo masa abincin a wajansa,har sai da aka kawo wani kwanon na wadda ta fasha wancan kwanon,sai Annabi s.a.w ya amshi kwano mai kyau ya sa aka maida mata shi kuma kwanon fasashshen aka baima wadda ta fasa"*.
@صحيح البخاري.
Saboda da nuna adalci tsakanin matansa da kuma kyautata zaman tare a tsakaninsu,wanda wannan shine abinda aka rasa acikin mafiya yawan gidajen auran mu.
●Hakika Annabi s.a.w ya kasance mai yin shawarane da matasa acikin al'amura masu yawa,ya isa misali abinda ya faru a Sulhul Hudaibiya,lokacin da Annabi s.a.w ya umarci Sahabbansa su yanke abinda Hadayarsu kuma su aske gashin kansu, amma basuyi ba saboda abinda yayi masu tsanani akan su koma basu shiga Makkaba basu san hakan,sai Annabi s.a.w ya shiga wajan matarsa Ummu Salma acikin Shemarsa bai fito daga wajantaba face sai da ta bada shawarar da ta kawo maganin wannan matsala ga dukkan musulmai baki daya,sai Annabi s.a.w ya fita yayi aski kuma yanka hadayarsa,sai kowane Sahabi ya fita yayi aski yayi yanka kamar yadda Annabi s.a.w yayi,sai matsalar ta kau da shawarar matarsa R.A
●Wata rana Nana Aisha tayi fishi da Annabi s.a.w sai Annabi s.a.w yace da ita:
(Shin kin yarda Abu Ubaida bnul Jarrah yayi hukunci a tsakanin mu?? Sai tace a'a wanna bawan Allah bazaiyi min hukunci tsakani na dakai, sai yace:
(To umar R.A yayi hukunci a tsakanin mu) sai tace: a'a ina tsoran Umar R.A sai yace:
*(Shin zaki yarda da hukuncin Abubakar babanki R.A??)*
Sai tace:Eh
To acikin mu wanene zai iya hakan???
Annabi s.a.w,Allah ya hadamu da shi a aljanna madaukakiya.