SIRRIN KALMAR SHAHADA DA ISTIGHFARI
شيخ الإسلام ابن تيمية رحمه الله:
Yana bayani akan sirrin dake cikin Kalmar shahada wato:
[ لا إله إلا الله ]
Da kuma Sirrin ISTIGHFARI wato:
{ الإستغفار }
Da kuma alaqar dake a tsakaninsu sai yake fada game da fadin Allah Madaukakin Sarki:
﴿ فَاعْلَمْ أَنَّهُ لَا إِلَٰهَ إِلَّا اللَّهُ وَاسْتَغْفِرْ لِذَنبِكَ وَلِلْمُؤْمِنِينَ وَالْمُؤْمِنَاتِ ۗ ﴾
(Sabõda hakaa ka sani, cẽwa bãbu abin bautãwa fãce Allah, kuma ka nẽmi gãfara ga zunubin, ka, *"kuma sabõda mũminai maza da mũminai mãtã")*.
Sai yace:
*Lallai tabbatuwar Tauheedi yana kore dukkan shirka gaba daya
Haka kuma yawaita Istighfari yana kore sauran zunuban da ba shirkaba.
Mafi yabo da zikirin Allah shine fadar:
{لا إله إلا الله }
Kuma mafi girman Addua da neman gafarar Allah,shine bawa yace:
[استغفرالله ]
*Allah ya umarcemu da Tauheed da kuma nemawa kanmu gafara wato istighfari da kuma sauran yan uwanmu masu imani baki daya*.
مجموع الفتاوى ( 11/697 ) .
Ya Allah ka gafartawa dukkan musulman duniya baki daya ka kuma tabbatar damu akan Tauheedi da aqida mai kyau irinta Annabi s.a.w