DAGA ZUCIYATA 03


DAGA ZUCIYATA 03

Na san ni mai laifi ne
Ka san ni mai laifi ne
Kin san ni mai laifi ne
Kun san ni mai laifi ne
Kuma kowa na duniya yana laifi.

Na san ni mai zunubi ne
Ka san kai mai zunubi ne
Kin san ke mai zunubi ne
Kun san ni mai zunubi ne
Kuma kowa na duniya yana zunubi.

Na san na yi kuskure
Ka san ka yi kuskure
Kin san na yi kuskure
Kun san na yi kuskure
Kuma kowa na duniya yana kuskure.

Kada duniya ta ruɗe ka
Kada abokai su ruɗe ka
Kada kuɗi su ruɗe ka
Kada zuciya ta ruɗe ka
Idan ko har ka yi hakan ka bar hanyar gaskiya.

Ka yarda wani ya fi ka 
Ki yarda wata ta fi ki
Ka yarda wasu sun fi ka
Ka bi duk wanda ya fi ka
Idan har ka yi hakan kana kan gaskiya.

In har ba ka son kanka
Ta yaya za ka so waninka?
In har ba kya son kanki
Ta yaya za ki so wanin ki?
In har ba son kanmu ta yaya za mu so wasunmu?

In kace ban fa iya ba
To ai sai ko ka koya min
In ko ba za ka iya ba
Ka ga dole ka ƙyale ni
Tun dai ita rayuwa sai da gwadawa.

In kika ce ba kya sona
Sai ki bar ni da mai sona
In ko sam ba ki iyawa
Sai ki kuma daina to bina
Domin ita rayuwa sai da soyayya.

Kowa dai na da ra'ayi
Na san kana da ra'ayi
Ke ma kina da ra'ayi
Kowa ma na da ra'ayi
To akan me za a ce kada in zamo mai ra'ayi?

Nima jini ne a jikina
Jini ne ba ƙarfe ba
Zuciya ce a ƙirjina
Zuciya ba dalma ba
Domin nima ɗan Adam ne ba ƙarfe ba.

Zan ci gaba...

©️✍🏻
 Jamilu Abdurrahman 
    +2348185819176
Post a Comment (0)