DAGA ZUCIYATA 04
Ko na yi ko kuma ban yo ba
Za ace ban yi dai-dai ba
Komai na yi wai na yi ƙwaɓa
Komai na yi wai ban caɓa ba
Sai kace ni ne na auri asara.
Nima fa ɗa na Adam ne
Nima fa ina da idanu ne
Nima ina fa da hanci ne
Nima ina fa da ai kunne
Nima ina da duk abin da kowa yake taƙama da shi.
Kamar yadda kake son kanka
Haka nima nake son kaina
Kamar yadda kike son kanki
Haka nima nake son kaina
Kamar kowa ni ma ina son kaina.
Kana so kai ka ji daɗi
Kina so ke ki ji daɗi
Ku sha madara mai garɗi
Da ɗanɗanon duk wani daɗi
To menene yasa ni ban cancanci hakan ba?
In har ma laifi ne na yi
Me ya sa za ku kyare ni?
Madadin ku nusar da ni
Shi ne sai kuma ku tsane ni
To menene ribar hakan don Allah?
Iyaye duk ku yi nazari
Shugabanni ku yi nazari
Malamai ku yi nazari
Manyanmu duk ku yi nazari
Shin matsalar ta ina take a sassan mu?
In Allah ya maka ni'ima
Burinka ka guji al'umma
In Allah ya jarrabe ka
Sai ka nufo gun Al'umma
Ta yaya ita al'ummar za ta ci gaba?
Ka ce ni wai yaro ne
Aikin ga wai na manya ne
Manya a cikin dukka mutane
Wai ni na gaza in gane
Bayan kuma kullum duniya ni ake cuta.
Ku sani Allah na nan
Ku sani tsufa na nan
Ku sani mutuwa na nan
Ku sani lahira na nan
Ku sani ranar tsayuwa ita ma na nan.
Rabbana ka yafe mu
Rabbana ka kare mu
Rabbana ka shirye mu
Rabbana ka cece mu
Rabbana ka kawo mana ɗauki da gaggawa.
©️✍🏻
Jamilu Abdurrahman
(Mr. Writer)
+2348185819176
Haimanraees@gmail.com