DOMIN RAGE YAWAITAR FYAƊE

Kaɗan Daga Cikin Abubuwan Da Idan Iyayenmu Mata Suka Kiyaye Insha Allah Za A Samu Sauƙin Yawaitar Fyaɗe

Daga Abba Adam Isah

1. Ki gargadi 'yar ki kada ta kuskura ta
zauna a cinyar wani, koda kanin babanta ne
ko Almajirin gidansu.
.
2. Kada ki dinga canja kaya a gaban
'ya'yanki wadanda suka kai kamar shekara
biyu. Ki dinga cewa su fita.
.
3. Kada ki yarda wani babban mutum ya
dinga kiran 'yar ki da "Mata ta" ko
"Amarya ta" dds.
.
4. Idan 'ya'yanki suna wasa da wasu yaran,
ki dinga lura wane irin wasa sukeyi. Saboda
wasu yaran suna wasa da al'aurar junansu.
.
5. Kada ki matsawa 'yar ki zuwa wajen
wanda ba ta so ta je wajensa. Kamar
wani me siyar da kayayyaki ko
makamancinsu.
.
6. Ki saka lura sosai idan kika ga dan ki ko
'yar ki sun shaqu da wani mutum a waje
kuma suna son zuwa wajensa.
.
7. Kada ki bari dan ki ko 'yarki su dinga
yawo ba riga ko wando a cikin gida balle su
fita waje.
.
8. Idan kin yiwa 'yar ki kwalliya, to ki gaya
mata iya gidajen da za ta shiga.
Kuma daga nan ta dawo gida. Kada ta zauna
a rariya ko shige-shigen gidaje.
.
9. Idan ki ka ji an yiwa abokin dan ki ko
kawar 'yarki wani abu mara dadi, to kema ki
binciki na ki sosai. Ki tuhume shi.
.
10. Idan 'ya'yanki mata sun fara girma, ki
koya musu yadda ake kula da jini. Da yadda
ake kula da budurci da hadarin kawar da
shi. In ba haka ba zata fara koyar munanan
dabi'u a wajen kawaye.
.
11. Ki kula da irin kayan wasan da yaranki
suke amfani da su. Kamar yartsana me
hoton tsiraici da makamantansu.
.
12. Ki koyawa 'yar ki me shekara uku yadda
ake wanke muhimman gurare ajiki, har da
kirji kuma ki gaya mata kada ta bari kowa ya
ta6a mata nan wajen da nan wajen.
.
13. Ki tabbatar duk wani hoto ko abin
amfani wanda zai 6ata tarbiyyar yaro kin
nisanta shi da inda yaranki za su gani.
.
14. Duk sanda 'yarki ko danki ya kawo miki
karar wani babba ya cire masa
kaza ko ya ta6a masa kaza, to kada ki dau
mastalar da wasa.
.
A bi duk matakan da suka dace don
tabbatar da
abinda ya faru.
.
15. Ku tuna tarbiyya tana farawa ne daga
gida

 Allah Ubangiji ya ƙara shirya mu ya kuma shirya mana zuri'ar mu ya tsarkake mana zuciyoyin mu Amin.

Post a Comment (0)