GIRMAMA SHUGABA

Girmama Shugaba
Ibn Abi Asim ya qulla babi a littafinsa mai suna (السنة) ya ce:
 (باب في ذكر فضل تعزير الأمير وتوقيره)

sannan ya kawo hadisi da isnadinsa zuwa ga Muazu Dan Jabal (رضي الله عنه) ya ce: manzon Allah (SAW) ya ce: 

"خمس من فعل واحدة منهن كان ضامنا على الله عز وجل: من عاد مريضا أو خرج مع جنازة أو خرج غازيا أو دخل على إمامه يريد تعزيره وتوقيره أو قعد في بيته؛ فسلم الناس منه وسلم من الناس"

Ma'ana

"Abu biyar, wanda ya aikata daya daga cikinsu Allah ya lamunce masa.
- Wanda ya je dubiyar maras lafia
- Wanda ya raka gawa zuwa maqabarta
- Wanda ya fita zuwa jihadi
- Wanda ya je gun shugabansa da niyyar ya girmamawa da mutuntawa
- Ko kuma ya zauna a gidansa har mutane suka tsira daga sharrin sa shima ya tsira daga sharrinsu.

Baya ga Ibn Abi Asim, Ahmad ya fitar da hadisan da shi da Dabarani da Abu Ya'alah da Ibn Khuzaima da Ibn Hibban. Albani ya inganta shi a (ظلال الجنة)

Allah ka sa mu dace

Post a Comment (0)