FAƊAKARWA GA BARIN SHAN GIYA

*FAĎAKARWA GA BARIN SHAN GIYA.*


Shaye-Shaye, wato shan dukkan wani kayan maye da zai gusar wa mutum da hankali ya fitar da shi daga hayyacinsa. Allah Yana cewa:

*”يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا إِنَّمَا الْخَمْرُ وَالْمَيْسِرُ وَالْأَنْصَابُ وَالْأَزْلَامُ رِجْسٌ مِنْ عَمَلِ الشَّيْطَانِ فَاجْتَنِبُوهُ لَعَلَّكُمْ تُفْلِحُونَ“*

Ma'ana: *“Ya ku waɗanda suka yi ĩmãni! Abin sani kawai, giya da cãca da refu da kiban ƙuri´a, ƙazanta ne daga aikin shaiɗan, sai ku nĩsance shi, wa la´alla ku ci nasara.”* (Al-Maa'idah: 90).


Dukkan wani abin da zai sa mutum mayè, buguwa ko fitar da shi daga hayyacinsa haramun ne. Wannan ya shafi kowane nau'in kayan shaye-shaye kamar su sigari, ko da ci ake yi, ko sha, ko shaqawa a hanci, ko zuqa da baki, ko allura ko ma ta kowace hanya, dukkansu haramun ne sai mu nisance su. 

Dukkan wanda yake shaye-shayen kwayoyin maye, to fa babu laifin da ba zai iya aikatawa ba, kasancewar ya fita daga tsarin da Allah Ya halitta sa a kai. 


Allah Ya sa mu dace kuma Ya kare mana imaninmu. 
..
..
*✍🏾Ayyub Musa Jebi Giwa.*
*(Abul Husnain).*


Daga Zauren 
*🕌Irshadul Ummah WhatsApp.*
*08166650256.*

Telegram:
https://t.me/irshadulummah

Post a Comment (0)