MUN SANI AMMA BA MA AIKI DA SHI

#MUN SANI AMMA BAMA AIKI

 
قال ابن القيم(رحمه الله)
Yana cewa:
Wata yarinya ta rasu sanadiyyar Annoba,sai Mahaifinta ya ganta a mafarki,sai yace da ita:
*"Yake Æ´a ta ki bani labari game da lahira*
sai tace:
_Hakika anyi mana baiwa akan wani abu mai girma,hakika mun sani amma bama aiki....._

Ina rantsuwa da Allah, wallahi yin *TASBIHI* (Wato fadar SUBHANALLAH) guda daya ko *RAKA'A* guda daya a littafinka aiyukana,ita tafi soyuwa agareni fiye da duniya da abinda yake cikinta".

Hakika wannan yarinya ta fadi wata magana mai tsada da mafi yawan mutane bamu fahimci abinda take nufi ba.

Tana nufin:-
Musan fadar;
*"سبحان الله وبحمده"*
_SUBHANALLAHI WABIHAMDIHI_ Sau dari yana kankare mana zunubai gaba daya ko da sun wuce yawansa ya akai kamfar teku,amma sai yini da darare masu yawa su wuce bama fadar wannan zikiri.

Kuma mun san yin raka'a guda biyu na sallar wallaha,yana daidai da sadaka 360,amma sai mu dauki tsawon lokaci bamayin sallar wallaha.

-Kuma hakika mun san yin azumin yini guda na nafila dan Allah,Allah yana tseratar da shi daga shiga wuta na tsawon tafiyar shekara 70,amma mafi yawan mu bamayin azumin nafila.

-Kuma mun san wanda ya tafi duba marar lafiya,mala'iku guda dubu 70 sukeyi masa rakiya kuma suna nema masa gafara,amma kadaine daga cikin mu suke zuwa duba marar lafiya.

-Kuma mun san cewa yin sallar gawa da rakata har a binneta,mutum yana damun ladar Qiradi guda biyu,kuma kowane Qiradi yana daidai da dutsen uhudu,amma mafi yawan mu bama kwadayin yin hakan da samun ladar.

-Mun san cewa dukkan wanda ya ginawa Allah masallaci,koda masallacin na itaceni shima Allah zai gina masa gida a cikin Aljanna,amma mafi yawan masu dukiyar mu basa aikata hakan.

-Mun san cewa wanda ya taimaki matar da mijinta ya mutu da masu karamin karfi,yana da matsayin mai jihadi wajan daukaka addinin Allah,kamar mai yin azumine acikin yini mai raya dare da ibada,amma mafi yawan mu bamu damu da taimakonsu ba.

-Mun san cewa duk wanda ya karanta harafi guda na alqurani yana da ladar kyakkyawan aiki guda goma,amma baka samun masu karatun alqurani sai mutane kadan daga cikin mu.

-Sun san cewa aikin Hajji karbabbiya bata da wani sakamako awajan Allah sai gidan Aljanna,kuma mai aikin hajji zai dawone kamar ranar da mahaifiyarsa ta haifesa,wato an gafarta masa dukkan zunubansa,amma zaka ga mutane da dama Allah ya basu iko amma basu kokarin tafiya sauke farillar aikin hajji.

-Kuma mun san mafi daukakar samun matsayin mai Imani shine yin sallar nafila acikin dare,kuma Manzon Allah da Sahabbansa R.A sun kasance basu bari yin sallar dare,amma mafi yawan mu bamayin sallar dare.

-Kuma mun san Alqiyama tabbasce babu kokwanto akanta,kuma lallai Allah zai tayar da dukkan wanda ya mutu dan yimasa hisabi,amma bama yin Guziri dan wannan tafiya mai tsawo.

-Mun kasance muna bunne mamatanmu amma bama yin guzirin kwanciyar qabari.

-Kuma mun san wanda ya koyar da wani alkhairi ko ya tunatar da shi,yana da irin ladar abinda ya aikata,amma bama kokarin yin hakan.

Dan haka mu isar da wannan sako ga yan uwan mu ko Allah zai sanya mu zama sanadiyyar su aikata ko su gyara kusakuransu.

Allah ya shiryar da mu hanyar madaidaiciya.

Post a Comment (0)