HANYAR KAWAR DA NANƘARWA


SIRRIN MALLAKAN MIJINKI

Hanyar Kawar Da Nankarwa (Strech Mark)

Nankarwa shine irin wani zane da yake fitowa a cikin mace ko da zaran ta fara haihuwa ko kuma in tayi kiba, a cikin mace ya kan fito ya sanya fatar cikin duk ta yamutse.

Zaki nemi wadannan abubuwan kamar haka;
* Man Kadanya
* Man Zaitun
* Lemun tsami

Bayani; ki hada man kadanya da man zaitun guri guda, ki matsa lemun tsamin akan man, amma ba da yawa ba, ki juya sosai har ya hade, sannan sai ki dunga shafawa a wajeb da zane yake, kuma zaki dunga yine akai-akai har Allah ya kawo bacewarsa.

Wabillahi Taufiq.


Rubutawa: Abu Imam (Auwal Abdullahi)

Gabatarwa: Abu Imam (Auwal Abdullahi)


 Zauren Macen Kwarai

Ga masu buqatar shiga Zauren Macen Kwarai sai a turo da cikakkiyar sallam tare da cikakken suna da Address ta wannan Number +2348036692586,08062828025 a WhatsApp.
Post a Comment (0)