INA MAFITA?


*INA MAFITA*!!???

_Lamarin kullum karuwa yake yi bayan duk tanadin wahala da bala'oin dake cikin wannan lamari. Manya sun dauki zina a matsayin abin ado, yara ma haka, Kai hatta matan Aure da mazan Aure ma. Gashi kullum Aure ake a cikin mutane amma kullum abun karuwa yakeyi. Wannan kadai bai isa ka fahimci wannan aiki annoba bane? Shin kunsan illan da zina ke haifarwa mutum kuwa? Kun san illan da take haifarwa unguwa da gari kuwa? Lalle inda mutane sun sani bazasu kusanci aikata wannan laifin ba. Lalle ita ba mai aikatata a lokacin face sai an cire rigan imani a jiki nai, A cikin jahannama ma mazinata masifa ne ga sauran yan'wuta. Dukkan bala'in dake cikin wuta ace anan ma kazama abunda zaka dami sauran yan ciki anya kuwa wannan karamin lamari ne? Duk wanda ka ganshi da dabi'ar lalata ya'yan wasu to zakaga yafi kowa zakewa wurin killace nashi, amma kashi aikin gama ya gama ai. Mudai a yau wannan aiki ( *Zina*) tazama abin ado a cikin mutane._

_Watsi da karantarwan addini da tarbiyyan musulinci gami da wancakalarda shari'an musulinci yana daga cikin ababenda suke kara wannan batu a cikin al'ummah. Shin wani gudumawa zaku bada kan wannan matsalar? Shin mi kuka fahimta gami da ita bayan abubuwan da na bayyana? Shin kanada karin bayani akai? Ina sauraronku akan wannan batu_
Post a Comment (0)