*JAGORA DA WANDA AKE JAGORANTA*
^^^^^^√√√√^^^^^^
Allah madaukakin sarki ya raba ayyuka kuma yaba kowa NASA:
1- *Shuwagabanni* su riqe nasu suyi qoqarin saukewa, domin Allah zai tambayesu game da nauyin daya daura masu.
2- *Wad'anda ake shugabanta* su riqe nasu suyi qoqarin saukewa, domin Allah zai tambayesu game da nauyin daya daura masu.
Kada wani ya shiga aikin wani!
Duk wanda ya shiga aikin wani, ko yayi sakaci wajen zartar da nasa aikin, lallai ya sa'bawa Allah madaukakin sarki.
Shugabanci abune mai tsananin wahala, kuma lallai akwai hisabi tsakanin shuwagabanni da mabiya.
Duk wani shugaba wanda yayi amfani da jagorancinsa ko qarfin mulkinsa ya tsangwamawa wad'anda yake jagoranta, lallai zai tarar da hukuncinsa a wajen ubangijinsa.
Tabbas haqqi ne ga shugaba ya tsarewa al'ummarsa ababe kamar haka:
*(1) Rayukansu*
*(2) Addininsu*
*(3) Dukiyoyinsu*
*(4) Hankulansu*
*(5) Mutuncinsu*
Da sauransu.
Allah madaukakin sarki bai sahhalewa wani mabiyi yayi taratsi da fito na fito ga shuwagabanni ba.
Saidai ya daura masu nauye-nauye wajen mu'amalantar shuwagabanninsu kamar haka:
_(1) Yi masu 'da'a cikin dukkanin abinda yake daidai_
_(2) Haquri game da zaluncinsu idan azzalumai ne._
_(3) Yin nasiha garesu a boye ta hanyar girmamawa da tausasawa._
_(4) Yi masu addu'ar gyaruwa da shiriya da samun nasara a cikin jagorancinsu._
Lallai akwai buqatar mu kyautata domin mu sami yardar Allah, mu daure muyi riqo da tafarki madaidaici domin samun tsira duniya da lahira.
Allah ya datar damu da abinda yake so kuma ya yarda dashi.
_Daga_:
*Abul-Mustapha, Sulaiman Uthman Al-athary*