KANGANA RANAUT


KANGANA RANAUT

Ga Kangana Ranaut shugabar duk 'yan gagara
Ba kya son raini ke ɗin kuma yau kin shahara
Ba kya ɗaukar wulaƙanci gashi yau kin faskara
Jajircewarki ta sa ki ga shi yau kin gagara
Karfin zuciyarki ta sanya yau kin wuce hantara
Ah! Mai girma Kangana ga waƙarki yau tana jira.

Kyakkywar Jaruma doguwa mai ƙirar damisa
Duk wani tsuntsu da ya ganki dole ya haura bisa
Ƙwararrar jaruma mai taƙama ko da babu busa
Maƙiyanki gaba ɗaya kin yi musu ƙusa
Zafi ko barkono sai dai ya yi miki tausa
Me jiji da kai kin zarce ayi miki ƙusa Kangana

Ko da an ƙi ko da an so kin yi musu nisa
Komai girman ƙato ke ɗin ba kya jinsa
Macen farko a Bollywood da ba ta kissa
Ga darakta ko jarumi domin ɗaukar fansa
Kin yi mun gani ke ce uwar sambisa
Cau! Cau! Cau! Cau! Cau! Cau! Cau! Cau! Ina yi miki jinjina

A daka, a raya, a raba sai kalwa
Wani naman kai dai malam je ka gun giwa 
Wani labarin in ka na so ka je wajen kurma
Wani tarihin in kana so ka je garin bama
Wani al'amarin dai ganinsa sai a fagen fama
Shege shi ka fasa ɗan halas sai dai ya mutu yana fama.

Jamilu ne katibin nan ke yi miki jinjina
Dakyau jaruma bango da ke aka jingina
Watarana matan Bollywood da ke za su dangana
Ko yanzu in kana so jeka ka tambaya
Ita ce ƙwal kowa ya sani ba ma zancen fariya
Na barki lafiya Kangana uwar 'yan kangara.

©️✍🏻
 Jamilu Abdurrahman 
    +2348185819176
Haimanraees@gmail.com 
Post a Comment (0)