MU IYA BAKIN MU!


*MU IYA BAKINKIN MU!!!*


 *Sai ka Rasa Wa Ake Wa Qorafin?!*

Mahaliccinmu dai shi ya farlanta mana azumtar ramadana, kuma shi yayi alqawarin bada ladansa, amma mu kan manta da wannan, a maimakon mu shagala wajen bauta dan ganin azumin mu ya inganta, sai muka bige da yawan qorafe qorafe, da yawan fadin azumin nan akwai wahala, azumin nan ji nake kamar na karya shi, azumin nan kaza da kaza, da sauran maganganu marasa amfani da suke nuna gajiyawa da qorafi da mita irin na dan adam, wasu har izgilanci suke da hakan!

mu kiyaye, mu kame bakin mu da jinmu da ganinmu, muyi haquri, mu jure, mu tina dinbin ladan mai azumi a wajan Allah, sai mu dace.

👌Wannan nasiha ce gare mu, Azumi ibada ne ita kuma ibada sai anyi haquri an tsarkake niyya, sannan take inganta har a samu ladanta!
*Allah ya karbi ibadun mu, Ameen.*



✍🏻 *Habeebatus Sunnah*
Post a Comment (0)