KO KA SAN ƘASA ZA TA YI KUKA A DALILINKA?

KO KASAN ƘASA Zata YI KUKA A DALILINKA?? 


Ƙasa tana kuka wa bawa, wanda kukanta ga ɗan Adam Kala biyu ne, wani tayi kukan rabuwa dashi, wani kuma tayi kukan takaicin nauyi da ya ɗora mata na zunubansa. 

    Dawud bin Ƙais Allah ya masa rahama yake cewa, Na ji Ibnu Ka'ab yana cewa "lalle kasa tana kuka wa bawa, sannan kuma tana kuka akan bawa, tana kuka wa bawa idan ya kasance yana aikata aikin alkhairi akanta. Tana kuka kuma akan bawa idan ya kasance yana aikata zunubai akanta, ya nauyayata da zunubansa. Sannan sai ya karanta fadin Allah (Sammai da Ƙassai basu yi musu kuka ba saboda mutuwarsu, hakanan kuma basu kasance cikin waɗanda za'a jinkirta musu ba). 
حلية الأولياء ٣/٢١٣

Sannan Mujahid yace, "Mumini bazai mutu ba face sama da kasa sunyi kuka da mutuwarsa har tsawon safiya guda 40". 
    Sai Dawud bin Ƙais yace masa: Shin yanzu kasa tana kuka?? Sai yace : shin kana mamaki ne?? 
    Meyasa kasa baza tayi kuka ba saboda rabuwa da bawan da yake rayata da ruku'u da sujjada?? 
   Meyasa sama baza tayi kuka ba akan rabuwa da bawan da kabbarorinsa da tasbihinsa yake acikinta kai kace karan kukan tawagar kudan zumane". 
تفسير ابن كثير ٤/١٧٩
Imam Al-Ada'u yake cewa "Babu wani bawa da zai yi sujjada awani wuri face wannan wurin ya bada shaida akansa ranan qiyama, kuma wurin yayi kuka ranan mutuwar wannan bawan"

الدر المنثور ٧/٤١٣

#ZaurenFisabilillah

Telegram : https://t.me/Fisabilillaaah

Post a Comment (0)