Ku nemi waraka ta hanyar karanta Fatiha

KU NEMI WARAKA TA HANYAR KARANTA SURATUL FATIHA

Saratul Fatiha itace sura mafi falala kuma mafi matsayi da albarka acikin surorin Alqur'ani Mai girma,surace da ta kunshi ma'anar alqurani da sakon da alqur'ani yake da shi a dunkule,kuma surace da Manzon SAW yace mata mai waraka.

Ana samun waraka daga dukkan kowane rashin lafiya ta hanyar karanta SURATUL FATIHA,kamar yadda hakan ya faru a kissar sahabban Manzon Allah SAW,kuma Annabi SAW ya tabbatar da hakan.

SURATUL Fatiha waraka ce ga kowace rashin lafiya tare da ikon Allah,sannan bisa karfin imani da yakinin mai neman waraka .

الشيخ ابن عثيمين رحمه الله تعالى: 
Yana cewa:-
"Kowace rashin lafiya kake fama da ita ,to ka nemi waraka ta hanyar karanta suratul Fatiha,saboda Manzon Allah SAW;-
*(Wa ya sanar da kai SURATUL Fatiha waraka ce?)* sai Manzon Allah SAW ya saki maganar warakar akan kowace rashin lafiya.

Dan haka kowace rashin lafiya ka karanta mata SURATUL FATIHA zaka samu waraka da ikon Allah,amma sai ka hada da gaskata Manzon Allah SAW da karfin yakini
@شرح البلوغ (52/2)

          Allah ne mafi sani


*-Ya Allah ka baima dukkan musulmai marar sa lafiya ka basu lafiya da tsawon rayuwa mai albarka-*.

Post a Comment (0)