KUNUN ALKAMA


KUNUN ALKAMA

yin kunun alkama bashida banbanci da yanda akeyin kowanne irin kunun saidai akwai gagarumin babanci wajen ciko nonon mace domin shi wannan kunun koda mace tana shayarwa zata iya shansa saboda zai temaka mata koda ta gama shayarwa nononta bazasu kankance su zama kananaba amma ba aso mace me cikin tarinka shansa...

yanda zakiyi alkamar zaki samu ki hadata da farar shinkafar tuwo da aya danya saiki jikasu zaki iya saka gyada danya saiki kayi markadensu idan an markada saiki tace kiyi kunu dashi kamar dai yanda kika saba dama kunu ko koko zaki iya saka kayan hadi don yayi miki kamshi kuma wadansu suna zuba madara aciki lokacinda za asha adadin yawansa kuma duk yanda kikeso zakiyi...






YANDA AKE KUNUN ALBASA


ga yanda zakiyi
ki samu albasa ki yankata sannan ki dafata da zallan ruwa
har sai ruwan yayi baki sai ki sauke ki tace albasar ki zubar saiki xuba xuma acikin ruwan sannan ki zuba garin gero ko kamu da garin alkama sannan ki xuba madara paek ko.nono ko kuma ki saka garin madara luna 
ki mayarshi kan wuta kina juyawa idan kin tabbatar ya zama.kunu saiki saukar dashi ki rinka sha da duminsa kuma kadan zakiyi yanda zaki iyasha gaba daya idan ya kwana zai iya baci kuma zakiyi bayan kwana daya saiki sake sannan akalla ana bukatar kiyi kamar sau goma




HASKEN MA AURATA
littafin auwal azare

Post a Comment (0)