*SIRRIN MALAKAN MIJINKI*
*Hanyar Mallaken Zuciyar Matanka*
Allah ya halicce mu ne don mu bauta masa kuma shi ne ya sanya soyayya da sha’awa a tsakaninmu.
Saboda haka mazajen da suke son ganin sun mallaken zuciyar matansu ko kuma samun zuciyarta ba tare da wata mishkila ba, ga wasu hanyoyi kamar haka;
1. TSARI: Duk wata ‘ya mace tana son ta ga namiji mai tsari, ba wai tsari irin na magana ba. Abin da nake nufi da haka shi ne, namiji ya kasance yana da tsarin rayuwa mai kyau, ba mutum ya zama shashasha marasa kan gado ba.
2. KYAU DA KWALLIYA: Wasu matan suna son mutum mai kyau da kwalliya ba irin su wancan nanka ba, sau da yawa za ka ga mata suna soyayya da saurayi saboda tsabar kyau da Allah ya ba shi, da kuma iya kwalliya kamar É—awisu.
3. KALAMAI: Yana da kyau namiji ya zama ya iya kalaman da za su janyo hankalin matansa, rashin iya kalami kan janyo rashin masoyi. Maimakon haka sai ka zama tamkar É—an bora a soyayya. Dole ne ka kasance ka iya kalaman da zasu dunga burge matanka.
4. KIRKI DA KULAWA: Namiji yakan tafiyar da zuciyar ya mace dalilin kasancewa mai kulawa da kirki. Misali duk bayan wani lokaci ko sa’ar l, in baka tare da ita kana kiran ta. Musamman ma a irin wanan lokacin da wayar hannu ta zama ruwan dare.
Wabillahi Taufiq.
Rubutawa: *Abu Imam (Auwal Abdullahi)*
Gabatarwa: *Abu Imam (Auwal Abdullahi)*
*- Zauren Macen Kwarai-*
*. Ga masu buqatar shiga Zauren Macen Kwarai sai a turo da cikakkiyar sallam tare da cikakken suna da Address ta wannan Number +2348036692586,08062828025 a WhatsApp.*