KWAƊI DA SARKIN SU


KWADI DA SRKIN SU
GATANAN GATANANKU
Wai wasu kwadi ne suke zaune a cikin wani tafki cikin jin dadi da walwala, ba abin da suka nema suka rasa, idan sun gaji da wasansu cikin ruwa sai su tsallaka kan tudu su sha iska. Ba su damuwar kowa, kuma babu wani abu da yake damun su. Suna nan haka sai wasu daga cikinsu suka ce, ina amfanin zamanmu haka babu wani Sarki da zai rika mulkinmu, ba mu da wasu dokoki da za su tafiyar da tsarin rayuwarmu.

Allah kuwa ya amshi addu'arsu! Ana nan wata rana sai wani dan guntun reshen bishiyar da take bakin tabkin ya karye, ya fado kwatsam a gefen tabkin. Kwadi suka tsorata suka fada ruwa da gudu. Sai wasu daga cikinsu suka ce ai
Sarkin da suke roko a turo musu ne Allah ya turo musu. Kwadi na cikin ruwa suna jira su ji irin dokokin da Sarki zai shata musu, suka ji shiru, su kuma suna jin tsoron su matsa kusa da shi. Ana nan dai har wani mai karfin hali daga cikinsu ya matsa kusa da reshen itacen nan da ya fado, sannu-sannu har ya kai ga taba shi, icce bai motsa ba, har ya hau kansa, yana rawa, itace dai bai motsa ba. Da saura suka ga haka, sai duksuka fito suka haye kan reshen itace. Sai ya kasance koyaushe nan ne wurin zaman kwadi tare da sabon Sarkinsu. Sai dai kwadi ba su yi murna da wannan Sarki da aka turo musu ba, suka nuna sun fi son Sarki mai rai, mai motsi, wanda zai rika shata musu dokoki, kuma ya shimfida mulkinsa.

 Wannan buri na kwadi ya sa Allah ya yi fushi da su. Kwaram ran nan sai ga wani zalbe zai wuce ta wurin, sai ya ga kwadi da yawa bakin tabki, shi ke nan abin nema ya samu, dama wurin neman abinci zai tafi. Sai ya tsaya bakin tabkin nan ya rika kamakwadi yana cinyewa. Da kwadi suka ga zalbe ya dame su da kisa haka, ya hana su sakat, sai suka ce wannan wane irin Sarki ne aka turo mana. Mu dai mun fi son zamanmu na da. DA MULKIN
ZALUNCI GWAMMA ZAMA BABU
SARKI!
***

Kurungus kan dan bera, ba
don gizo ba da na yi karya...

 

 
Post a Comment (0)