SHARHIN FIM ƊIN ROWDY RATHORE

SHARHIN FIM ƊIN ROWDY RATHORE 


Rowdy Rathore fim ɗin Indiya ne da aka fitar a cikin shekara ta 2012 a cikin harshen Hindi. Fim ne na faɗa, rawa, soyayya da kuma barkwanci. Sannan wannan shirin maimaicin wani shirin harshen 
Telugu ne mai suna Vikramarkudu wanda aka fitar a shekara ta 2006. Na ba wannan shiri tauraro huɗu. 

MA'AIKATAN SHIRIN 

• Bada Umurni - Prabhu Deva
• Ɗaukar Nauyi - Sanjay Leela Bhansali & Ronnie Screwvala
• Rubutawa - Shiraz Ahmed
• Labari - K. V. Vijayendra Prasad
• Asalin Labari - S. S. Rajamouli
• Sautin Waƙoƙin Shirin - Sajid-Wajid
• Taken Shiri - Sandeep Chowta
• Horas da 'yan wasa - Santosh Thundiyil
• Tacewa - Aarti Bajaj
• Kamfanin da ya shirya - UTV Motion Pictures & 
Bhansali Productions
• Kamfanin da ya yaɗa - UTV Motion Pictures
• Ranar Fita - 1 June 2012
• Tsayin shiri - mintuna 143 
• Ƙasa - India
• Harshe - Hindi
• Kasafi - ₹45 crores
• Jimillar Kuɗin da ya kawo - ₹203.39 crores

Wannan fim an ɗauki mafi yawancinsa ne a Mumbai da kuma Hampi. A lokacin da aka saki wannan fim, wasu sun yabe shi wasu kuma sun kushe shi, amma duk da haka sai da wannan shiri ya kai matakin 'Blockbuster' a gida da kuma waje, hakan ya sa Rowdy Rathore ya zama ɗaya daga cikin fina-finan Indiya da suka fi kowanne kawo kuɗi a harkar kasuwancin fina-finan Indiya baki ɗaya. A wata zantawa da aka taɓa yi da Prabhu Deva, ya bayyana cewa in dai za yi na biyun shirin, to tabbas Akshay Kumar ne zai dawo domin ya taka irin rawar da ya taka a na farkon. Wannan ne ba bayyana mana cewa wataƙila a yi na biyun a nan gaba. 

LABARIN SHIRIN A TAƘAICE 

Shiva wani ɓarawo ne da ke zaune a garin Mumbai. Watarana sai ya faɗa soyayya da wata budurwa mai suna Paro wacce ita kuma ta zo ne daga Patna. Saboda son da yake yi mata, sai ya faɗa mata gaskiya dangane da sana'ar da yake yi, daga nan sai suka shirya akan cewa zai daina wannan mummunar sana'a saboda son da yake mata. Sai dai kafin a kai ga barin, sai ya yanke shawarar cewa bari yayi wata gagarumar sata tare da abokinsa mai suna 2G. A cewarsa, wai hakan zai bashi damar samun abin juyawa tun da zai bar sata 

A garin haka ne suka yi wa wata mata wayo a tashar jirgin ƙasa suka sace mata wani ƙaton akwati suna tunanin gwala-gwalai ne a ciki. Wannan ne ya zama sanadiyar haɗuwar Shiva da Chinki, wata ƙaramar yarinya wacce ita ce a cikin wannan akwati a maimakon alatun da suka zata. Yayinda aka buɗe akwati yarinya ta fito sai kuma ta fara kiran Shiva da suna Baba. Hakan ya sa wani jami'in ɗan sanda mai suna Vishal Sharma ya tursasa wa Shiva zama da Chinki tare da yi masa barazanar kai shi gaban hukuma in yazo bai yadda shi da yarinyar ba. To, shi kuma Shiva yana tsoron kada Paro ta ganshi da Chinki ta yi wani tunani na daban ya rasa ta. Daga baya kuma sai ya ga wani hoto wanda yake ɗauke da Chinki da kuma mahaifinta wanda kamanninsu ɗaya sak da shiva. Wannan yasa ya fahimci dalilin da yasa yarinyar nan ke kiransa da suna Baba. Daga baya sai aka bayyana mana cewa mahaifin Chinki ba kowa bane face wani gawurtaccen ɗan sanda wanda duk wani mara gaskiya ke shayi mai suna Vikram Rathore, a yayin yake faɗa da wani ɗan jagaliya domin ya nemo 'yarsa ne mota ta bige shi wanda hakan ya haifar masa da wani mummunan rauni ƙwaƙwalwarsa. Likitansa sai ya bayyana masa cewa akwai buƙatar ya bi a hankali domin raunin da ya samu na iya hallaka shi. 

Bayan wasu 'yan kwanaki, sai Shiva ya fara suƙewa da Chinki har ma ya fasa rikodar da take sauraren waƙar da mamanta ta rera a ciki. Washegari sai ya fahimci cewa mahaifiyarta ta jima da rasuwa. Ganin cewa abin da ya yi bai kamata ba, sai ya gyara mata rikodar ta sannan ya ci gaba da kulawa da ita yadda ya kamata. Cikin rashin sa'a kuwa sai Paro ta ga Shiva da Chinki, hakan ya sa ta yi tunanin cewa dama yana da 'ya ya ƙi faɗa mata. Don haka sai ta koma Patna cikin karayar zuciya. Ba a jima ba kuma, sai 'yan jagaliyan da ke neman Vikram suka ga shiva, a tunaninsu shi ne don haka sai suka far masa. Shiva da Chinki sai suka gudu inda a garin gudun ne suka haɗu da wannan mata da suka yi wa sata a tashar jirgi da kuma ɗan sanda Vishal waɗanda suka ce wa Shiva ya gudu da Chinki. Nan dai akai ta gurmuzu har aka kai wani wuri inda mugayen suka zagaye Shiva. Ashe duk wannan abu da ake yi Vikram na saman wani gini yana kallo, za a caka wa Shiva wuƙa kanan sai ga Vikram ya duro daga sama.

Shiva sa kowa da ke wajen sai suka cika da tsananin mamaki saboda ganin tsabar kamar da Shiva da Vikram suka yi. Daga nan sai Vikram ya kulle Shiva da Chinki a wani waje shi kuma ya hau faɗa da mugayen. Ko da yake ciwonsa ya tashi a yayin wannan faɗa, sai da ya hallaka mugayen gaba ɗaya. Bayan an kai Vikram asibiti ne sai Shiva ya fahimci cewa wannan matar da suka yi wa sata ashe jami'ar 'yar sanda ce mai suna Sipeta Razia Khan. A nan ne suka bayyanawa Shiva cewa wannan mutumi da suka yi kama da shi ɗan sanda ne mai gaskiya da ake girmamawa kuma sunansa ACP Vikram Rathore. Watanni shida kafin wannan lokaci, Vikram ya isa ƙauyen Devgarh a matsayin sabon ACP. Ashe a wannan ƙauyen akwai wani uban daba mai suna Baapji tare da ɗansa Munna waɗanda suke zalunta tare da tauye wa talakawa haƙƙinsu. Kai tsaye sai Rathore ya garƙame Munna bisa fyaɗe da ya yi wa matar Vishal Sharma. Amma saboda alfarmar da Baapji yake da ita a siyasa, sai aka fitar da Munna tare da cewa ma ai shi ɗin yana da taɓin hankali. Baapji sai ya shirya bikin murnar fitowar Munna inda Munna ya muzanta 'yan sanda a gaban kowa amma sai Vikram yayi wata dabara wacce ta zama sanadiyar mutuwar Munna. 

 
Washegari, sai ɗan uwan Baapji mai suna Titla ya kai wa Vikram farmaki inda ya soka masa wuƙa ta baya da kuma harbi da Vikram ɗin ya samu a kai Yayinda ya ceci wani yaron ƙauyen. Daga nan sai aka ɗauka cewa ya mutu, yayin da aka zo binne shi, sai aka ga yana motsi kuma yana numfashi, daga nan sai kowa da ke wajen ya yi alƙawarin cewa ba zai bayyana abinda ya faru ba. Daga nan sai ofisoshin suka taho da Vikram Mumbai domin su yi masa magani. 

Bayan Shiva ya gama jin wannan labari ne sai likita ya bayyana musu cewa Vikram ba shi da sauran isashen lokaci a duniya. Vikram sai ya roƙi Shiva da ya kula masa da Chinki. Shiva sai ya amsa tare da yi masa alƙawarin cewa shima Chinki 'yarsa ce. Daga nan sai Vikram Rathore ya mutu. 

Daga nan kuma sai Shiva ya sha alwashin ƙarasa aikin Vikram. Don haka sai ya maye gurbinsa kuma ya nufi ƙauyen Devgarh inda ya cinnawa masana'antar giyar Baapji wuta kuma ya raba wa talakawa hatsi da kuma kuɗaɗen da ya amshe musu. 
A ƙarshe dai Paro ta na fahimtar gaskiya kuma su shirya. A wani gagarumin faɗa da ake yi a ƙarshen shirin ne ake kashe Baapji, Titla da kuma sauran 'yan jagaliyarsu 

JARUMAN SHIRIN 

• Akshay Kumar - Shiva /Vikram Rathore (Dual role)
• Sonakshi Sinha - Paro
• Ananya Nayak - Chinki Rathore 
• Paresh Ganatra - 2G 
• Nassar - Baabji
• Supreeth Reddy - Titla
• Yashpal Sharma - Sipeta Vishal Sharma
• Saniya Anklesaria - yarinyar Sipeta Vishal Sharma 
• Meet Mukhi - yaron Sipeta Vishal Sharma 
• Gurdeep Kohli - Inspector Razia Khan
• Raj Arjun - Jagdish
• Mushtaq Khan - sirikin Baapji 
• Amit Tiwari - Munna 
• Anant Jog Minista 
• Darshan Jariwala - DGP Suraj Prakash
• Pooja Rawal - Mrs. Rathore 
• Shireesh Sharma - Mahaifin Paro
• Shruti Bapna - ƙawar Paro 
• Ashok Samarth - Babu
• Kareena Kapoor - Fitowa ta musamman. 
• Vijay - fitowa ta musamman 
• Prabhu Deva - Fitowa ta musamman 
• Maryam Zakaria - Fitowa ta musamman 
• Shakti Mohan - fitowa ta musamman 
• Mumaith Khan - fitowa ta musamman 
Waƙoƙin Shirin 

1. "Dhadang Dhang Dhang" 
2. "Chinta Ta Ta Chita Chita" 
3. "Aa Re Pritam Pyaare" 
4. "Chamak Challo Chel Chabeli" 
5. "Tera Ishq Bada Teekha" 
6. "Chandaniya (Lori Lori)" 
7. "Rowdy Mix" 

TSOKACI: A tsakanin fitowa kala biyu da jarumi Akshay Kumar yayi a cikin wannan fim, Vishal ya fi barkwanci kuma yana da sa'a sosai ga kuma wayo, yayinda shi kuma Vikram yake da ƙarfin damtse tare da rashin tsoro da kuma iya tsara magana. Wannan shi ne ya banbanta su. Amma ga wasu tambayoyi ga Prabhu Deva, masoyan Akshay Kumar da kuma duk wanda ya kalli wannan fim: bisa ga yadda labarin ya tafi, alamu sun nuna cewa Razia Khan tana sane ta bari Shiva da 2G suka saci akwatin da Chinki take ciki, to in haka ne me ye dalilin da yasa ta yi hakan? In kuma ba haka bane, to shi Sipeta Vishal Sharma tun da ya san Chinki, me yasa be karɓeta ya maida ita wajen mahaifinta ba tun da ya san inda yake? Shin sun yi hakan ne domin su rikita 'yan jagaliyan ko kuma dama sun san cewa Vikram Rathore zai mutu ne shi yasa suka yi hakan domin Shiva ya maye gurbinsa? In dama shiri suka yi, to shin ba sa tunanin cewa Shiva zai iya rasa rayuwarsa a sanadiyar haka? Shin ta yaya Shiva ya samu yarjewar hukumar 'yan sanda har ya maye gurbin Vikram Rathore? Ko suma dabarar yayi musu? In hakane, to kuma ta yaya zai ci gaba da zama a matsayin baban jami'in 'yan sanda shi da yake tsohon ɓarawo? Zan so jin ta bakin ku game da wannan. Nagode.

•----------•✬(✪)✬•----------•
 Jamilu Abdurrahman 
•----------•✬(✪)✬•----------•

    +2348185819176


Post a Comment (0)