MAGANA JARI CE
LABARIN KALALA DA KALALATU
Akwai wani mutum wai shi Kalala, yana da matarsa wadda a ke kira Kalalatu. Kalala Allah ya yi shi wani irin mutumin da ne, ba abin da ya fi da ki illa a yi masa abinci ya ci shi kadai. Da suna ci tare da wani makwabcinsa, sai makwabcin ya zama wani iri ne mai mita. Ya kan rika cewa Kalalatu ba ta iya miya ba, wai kullum miyarta daga ta cika gishiri sai ta cika ruwa.
Da Kalala ya ga tsegumin ya faye yawa sai ya bar kai abincinsa wurin makwabcin. Ya rika fita karauka yana nemo baki, yana kawowa gidansa suna ci tare.
To, Kalalatu ba ta kaunar wannan dabi’a ta mijinta, domin bisa ga misali, ran da Kalala ya yanka kaji biyu, iyaka Kalalatu ta sami cinya, domin duk Kalala zai kai wurin bakin da ya jawo ne su cinye.
Ta yi, ta yi ta hana shi wannan tabi’a, ya ki hanuwa. Saboda haka sau da yawa in ya ba ta dahuwa sai ta tsame rabi ta cinye, in Kalala ya yi magana ta ce ya kone ne, ko kuwa ta ce ta sauke ta shiga daki dauko kwano, kafin ta fito ta tarar kyanwa ta cinye rabi. Dalilai dai irin wadannan marasa kan gado ga su nan kullum Kalala na ta sha, amma saboda hakurin da Allah ya zuba masa ba ya cewa kome.
Ran nan, ko ina Kalala ya sami kudi sai ya tafi kasuwa ya nemo dakwalen kaji guda biyu ya sawo. Ya yiwo cefane ya kawo gida, ya ce wa Kalalatu ta soye kajin nan gaba daya.
Ta tashi, bayan ya fige ya gyara mata, ta sa tukunya ta shiga suya. Abu ga dakwalen kaji, duk kitse ya cika tukunya, sai wani abu su ke coi, coi, coi, in tana juya su. Duk kuwa kwadayi ya kama ta, da ma ga ta idonta idon nama sai ka ce kura sai yawu ke zuba dalala.
Ta sa dan yatsa ta dandana ta ji ko gishiri ya yi daidai, sai ta ji abin dadi ya kamo ta har ga keya, ta ce, “Kai, wadannan kaji yau suna shirin ganin wata irin gajerar suya. Amma dubi duk yawan kajin nan, rabona bai fi cinya ba daga cikinsu. Ka san dai halin mai gidan nan ya miskile ni.”
Ta ci gaba da suya kanshi na jifarta, ta yi kamar ta jure ta kasa, sai ta fara tsame tana ci, wai ta kau da mugun yawu. Kafin su soyu ta kusa cinye rabin kaza. Da ta sauke sai ta je ta gaya wa mijin sun soyu.
Kalala ya ce, “To, sai ki cire cinya guda, taki ke nan. Saura kuwa a ajiye, har in je in samo abokan ci.”
Kalalatu ta ce, “To.” Ta tafi ta cinye yar cinyar da aka ce ita ce tata, ta tsuguna tana kallon saura, sai mai ke zuba nash, nash.
Ta ruga wajen kofar zaure ta leka ko ta hango mijin tafe da bakin, ba ta ga kowa ba. Sai ta komo wajen kaji ta kura musu ido.
Sai ta ce, "Af, ashe ma fika fikai guda biyu sun kone tun dazun, bari ma in cinye na dayar don su zo daidai, kada mai gida ya gane." Sai ta fiffizge ta lakwame. Ta sake rugawa bakin zaure ta gani ko mijin na tafe, ba ta ga kowa ba.
Ta dawo ta tsaya bisa kwanon kaji ta ce, “Shin mai gidan nan zai zo dai? Ga kaji har sun fara yin sanyi. To, ni Kalalatu, yanzu in ya zo ya tarar wannan kazar duk na fiffige ta, ya tambaye ni in ce me? Ba abin da ya fi sai in cinye ta gaba daya, in ya zo in ce kyanwar gidan nan ta sace ta." Sai ta tsuguna ta cinye ta sarai, ta kwashi kasusuwa ta kai masai ta zuba.
Ta koma kofar zaure ta hanga, ba ta ga mai gida ba.
Da ta ga haka sai ta dawo, ta ce, “A bari ya huce shi ya kawo rabon wani. Bari in karkare cinye guda, kowa ya huta, in ya so in ya dawo kome ta tafasa ta kone.”
Sai ta kama kazar guda kuma ta lakume. Ta nufi randa ta debi ruwa ta kora, ta yi gyatsa, ta ce, “Madalla, kome ta ke zama ta zama.”
Ta zauna ke nan,
sai ga mai gida ya shigo. Ya ce wa Kalalatu, “Yi maza ki nika yaji ki barbada musu, kin san yanzu lokacin sanyi ne, ba abin da ya fi yaji amfani. Na manta ne in gaya miki ki nika yaji dazun. Yi hakuri, yau dai kin sha aiki.”
Kalalatu ta ce, ‘‘Ai ba kome, ku dakata mini dai kadan.”
Ta shiga daki tana ta shawarwarin abin da za ta ce wa mijin ya faru ga kaji. Tana can cikin daki,
sai Kalala ya dauki wuka ya nufi manika yana wasawa kararas, kararas, wai don ta yi kaifi ya sami ta yanka kaji kanana kanana, in an kawo.
Kalala na can na ta fama da washin wuka, sai Kalalatu ta ji ana sallama.
Ta yi farat ta fita bakin zaure wajen mai sallama, ta dube shi ta rike baki, ta ce, “Kai bako, kai ne mai gidan nan ya kirawo wai ku zo ku ci abinci?”
Bako yace, “I, Allah ya saka muku da alheri.”
Kalalatu ta ce, “Kai, tafi can, sakarai, ba ka san abin da a ke ciki ba. Kana tsammanin mutum mai hankali ya sa a yi masa abinci ya fita karauka neman abokin ci? In kana kama gabanka ka ruga, tun da wuri ka ruga. Ka ji shi can yana washin wuka, kunnenka guda zai yanke. Kullum haka ya ke yi, motsattse ne.”
Bakon nan, ko da ya saurara ya ji Kalala na washin wuka sai ya dafe keya ya zura a guje.
Kalalatu kuma ta ruga wajen Kalala, ta ce, “Ga irin jaye-jayen naka nan, ba ka san irin mutanen da ka ke jawowagida ba.
Kalala ya ce, “E? Mahaukaci ne?”
Kalalatu ta ce, “Mahaukaci mana, ko ba mahaukaci ba ne ai barawo ne, da barawo ko da mahaukaci ai duk tafiyarsu ke nan. Kajin da na barkada wa yaji, ko da ya gan su sai na ga ya yi wuf ya fizge, ya shafa a guje da su. Ga shi can ya mika, ya tasar wa kasuwa."
Kalala ya fusata, ya ce, “Allah wadan dan banza! Mutanen duniya ba wanda ke iya musu. Da ma ya bar mini ko da guda daya, ai da na sami ta kalaci. Dakwalen kajin nan duk ya cinye shi kadai? Bari in leka ko na hango shi, mu raba.” Sai ya ruga wajen zaure ya hanga, sai ga bakon nan can ya tattake da gudu kaca kaca kaca yana korar iska.
Kalala ya ce, “Kai abokina! Kai tsaya, don Allah ko guda daya ka ba ni! Wallahi su ke nan, mai dakina ko lasawa ba ta yi ba, ka dauke.” Bako ya yi kamar bai ji ba.
Kalalatu ta ce wa mijin, “Bi shi mana, a guje dai na san ba ya tsere maka.
Duk wahalan nan da na sha ta zama a banza, ko lasawa ban yi ba, ai ka san ka dauki alhakina.”
Sai Kalala ya runtuma a guje da wukarsa a hannu, ya bi bako yana kira, “Tsaya don Allah, daya kadai na ke so, na bar maka daya!”
Bako tsammani ya ke Kalala na nufin kunnensa daya kadai ya ke so ya yanka.
Ya waiwaya sai ya ga ya taso masa da wuka tsirara a hannu.
Saboda haka ya kara mai, ya dai yi wa Kalala fintinkau yana ji yana gani.
Da Kalala ya ga abin ba girma, sai ya juyo ya nufo gida da wukarsa a hannu, yana kutawa, yana Allah ya isa.
Da matar ta gan shi ya dawo yana zage zage sai ta tarye shi, ta ce, “Ya ba ka? Ka ga irin abin da na ke gaya maka nan tuni."
Kalala ya ce, “Ko tarad da shi na yi? Wannan akwai dan banza da gudu! Ga shi kamar tsoho, amma daya zura sai ganinsa a ke kamar ba ya taka kasa.
Bar shi ya je ya ci, ban dai yarda masa ba duniya da lahira. Allah ya isa. Daga yau ko sai yau, ba na sake kiran dan kowa ya ci abincina, tun da duniya ta sake. Mts, Allah wadai! Talaka dai ba aboki ne ba, ko ka so shi, ran biki kwa Bata.”