MATSALOLIN RASHIN SHA'AWA GA MATA

*SIRRIN MALLAKAN MIJINKI*

*_Matsalolin Rashin Sha‘awar Ya Mace_*

Matsalar rashin sha'awa ko rauni, akwai abubuwa wanda suke haifar da haka, wanda wani lokaci mace zataji bata jin dadi cikakke lokacin saduwa da mijinta.

Akwai wasu matsaloli kamar haka;

*1- Ciwon Kangarar Sha'awa:*
Ciwon kangarar sha’awa wani illane da shaidanu suke haifar ma mata. 
Yana iya kasancewa kama haka;
* Ciwon mara.
* Lalacewar ciki in ya samu.
* Mafarkin ruwa.
* Lalacewar maganar aure ga budurwa.
* Qin son yin jima’i.
* Bacin rai haka kawai.
* Rashin jin dadi yayin kwanciya.
* Mafarkin jira-jirai.
* Jin sha’awar wani wanda ba mijinki ba.
* Mafarki da ‘yar uwarki mace tana shafaki.

*2-Ciwon Baseer:*
Ciwon baseer wani ciwo da yake ma mace illa musamman wajen dauke ma mata sha'awa, kuma ko mace ta sha maganin sha'awa ko na kara ni'ima ba zai mata aiki ajiki ba, mafita shine ta nemi maganin baseer din.

*3-Ciwon Sanyi:*
Ciwon sanyi yana daga cikin abin da yake kawo ma mace matsala a wajen daukewar sha'awar mace.
Abubuwan da suke haifar da hakan sune;

* Qaiqayin gaba.
* Bushewar gaba.
* Daukewar ni’ima.
* Fitowar wari lokacin kwanciyar aure.
* Rashin cikakken dadi yayin gabatarda ibadar aure.
* Jin zafi lokacin kwanciya.

Wabillahi Taufiq.

Rubutawa: *Abu Imam (Auwal Abdullahi)*

Gabatarwa: *Abu Imam (Auwal Abdullahi)*

*- Zauren Macen Kwarai-*

*. Ga masu buqatar shiga Zauren Macen Kwarai sai a turo da cikakkiyar sallam tare da cikakken suna da Address ta wannan Number +2348036692586,08062828025 a WhatsApp.*

Post a Comment (0)