KULAWA DA TSAFTA

*SIRRIN MALLAKAN MIJINKI*

*_Kulawa Da Tsafta Shima Sinadarin Zaman Aure ne_*

*1. Tsaftar Tufafi:* Dole ne mace ta kula da tsaftar tufafinta da na ‘ya’yanta da na Maigidanta, mu sani cewa yawan kayan sawa wata baiwa ce daga Allah, amma tsafta da wanki da guga da fesa turare idan ana gida shi ake nufi da tsafta, da wannan ne mace zata amsa sunanta na mace.

*2. Tsaftar Wajen Girki:* Ana bukatar mace ta kula da tufafinta a lokacin da take girki dan haka shi zai qara tabbatar da tsaftarta. Saboda haka sai ta riqa amfani da qyalle ko tusmma na goge-goge, hakan zai taimaka qwarai wurin zama da kwalliyarta ko da tana girki kamar yadda bayani ya gabata, in kuma ta gama girkin sai tayi wanka idan akwai buqatar hakan amma bada ruwan qanzo ba!

Wabillahi Taufiq.

Rubutawa: *Abu Imam (Auwal Abdullahi)*

Gabatarwa: *Abu Imam (Auwal Abdullahi)*

*- Zauren Macen Kwarai-*

*. Ga masu buqatar shiga Zauren Macen Kwarai sai a turo da cikakkiyar sallam tare da cikakken suna da Address ta wannan Number +2348036692586,08062828025 a WhatsApp.*

Post a Comment (0)