MU KULA DA WANNAN


🌻 *MU KULA DA WANNAN* 🌻

Kuskure ne mu takaita ibadarmu acikin wannan kwanakin nan 10 na farkon watan ZULHIJJAH da yin Azumi kadai ba tare da yin sauran ibadu ba. 

Ba yin Azumi kadai ne kyakkyawan aikin da akeyi a cikin kwanakin nan 10 ba, kuma Kyawawan ayyuka basu takaita akan ibada guda daya ba tilo.

Zaka iyayin sadaqa, sallolin dare, Addu'o'i, Azkaar, Ihsani, sadar da zumunci, yad'a sallama, umarni da aikata kyakkyawa da kuma hani da aikata mummunan aiki da duk sauran ayyukan ibada .

Amma karka kuskura ka aikata wata ibada wacce babu umarnin Allah da na mazonta aciki, saboda Allah baya bayar da ladan aikin da bai sanya mutum ya aikata ba.

Dazarar kaga wata sabuwar Ibada, ko wata falala wacce baka taba ji ko saninta ba, to ka tambayi malamai kaji shin ya matsayinya yake? 

Kar Ayi awon gaba da imaninka, ka nutsu ka bautawa Allah Ubangijinka ta hanyar da yake so ba ta hanyar da kakeso ba. 

Allah yayi mana Albarka acikin kwanakin nan da ma rayuwarmu gaba dayansta, Yakarba mana ibadunmu kuma ya yarda da mu da ayyukanmu .

_*"Karku manta da ni acikin kyawawan Addu'o'inku."*_

✍🏻 *Idris M Rismawy*
Post a Comment (0)