RAYUWAR AURE


*SIRRIN MALLAKAN MIJINKI*

*_Rayuwar Aure_*
Akwai abubuwan da suke da matukar amfani wajen gyara zamantakewar kuma suna daga cikin abubuwan da rayuwa take bukata, wadannan abubuwan sune kamar haka:
1. Girki
2. Abinci
3. Tsafta
4. Zamantakewa
5. Kiwon Lafiya

Yar uwa ki sani kulawa da wadannan abubuwan yana sa mace ta samu rayuwar aure mai kyau domin kowane magidanci yana son ya ga matansa tana kulawa da wa'inan abubuwan.

*_Girki_*
Abinci ya zama dole a rayuwa, kulawa da shi yana gyara zamantakewa, rashin kulwa da shi kuma yana bata zamantakewa, dadin dadawa kuma Allah da ya haliccmu ya umarcemu da muci daga abubuwa masu dadi, Manzon Allah SAW ya tarbiyyantar damu a wurare da dama akan cin abinci, misalin hakan shine fadin Allah SWT:
“Yaku wadanda sukai imani kuci daga abubuwa masu dadi na abinda muka azurtaku dashi” (Baqara: 172)
Saboda haka ina fatan wannan taqaitaccen jawabi da zan gabatar zai zamarwa Uwargida ‘ci a hankali’ ko ‘ci ki qoshi kuma baki na marmari’ ko ‘hana mai gida fita’.



Wabillahi Taufiq.


Rubutawa: *Abu Imam (Auwal Abdullahi)*

Gabatarwa: *Abu Imam (Auwal Abdullahi)*


*- Zauren Macen Kwarai-*

*. Ga masu buqatar shiga Zauren Macen Kwarai sai a turo da cikakkiyar sallam tare da cikakken suna da Address ta wannan Number +2348036692586 a WhatsApp.*
Post a Comment (0)