SALAFUS SALEH 01

SALAFUS SALEH 
 
📌 (001) 
 
Abdullahi Ibn Mas'ud (Allah Ya kara Masa yarda) yace: 
 
"Dukkan wanda ya gyara tare da kyautata ɓoyen sa, to Allah zai kyautata tare da gyara masa bayyanan sa, duk wanda ya gyara alaƙar sa tsakanin sa da Allah, to Allah zai gyara masa alaƙar dake tsakanin sa da Mutane". 
 
Wannan fa'ida an ruwaito ta daga Magabata manya guda biyu, an ruwaito ta daga Ibn Mas'ud R.A da kuma Sufyanu Bn Uyaina Allah yayi musu rahama, kamar yadda yazo cikin waɗan nan littafai: 
Ibnu Abid-dunya a cikin Littafin Al-Ikhlas, da 
Al-Iman na Ibnu Taimiyah 
 
A taƙaice wannan Fa'ida tana koyar da mu abubuwa guda biyar: 
 
1- Aiyukan Bawa na ɓoye sun fi matsayi da daraja fiye da aiyukan sa na bayyane a wajan Allah.  
 
2- Allah yana yiwa Bawa sakamako gwargwadon yadda yayi aiki da kuma irin aikin sa.  
 
3- Mu kiyaye dokokin Allah a fili da ɓoye, wannan itace hanyar samun Aljanna mafi girma.  
 
4- Babbar alamar jin tsoron Allah itace: Mutum yafi kyautata aiyukan sa na ɓoye fiye da yadda zai yi su a fili a gaban jama'a. 
 
5- Ana samun matsayi da yardar Mutane ne ta hanyar kyautata alaƙa tsakanin ka da Allah. 

✍ ANNASIHA TV
(https://t.me/annasihatvchannel)

Post a Comment (0)