SHAWARWARI GA 'YAN MATA MASU NEMAN MIJI


*SHAWARA ZUWAGA YAN MATA MASU NEMAN MIJI*
.
.
*DAGA ZAUREN*
.
*MAJALIS - SUNNAH*
.
.
مجلس السنة
📓📔
+2349032091131
+237665087032
.
.
Yau 01/ 12/ 1441 wanda yayi dai-dai da 22/ 07/ 2020.
=
=
_Godiya ta tabbata ga Allah, muna gode masa, muna neman taimakonsa, kuma muna neman tsarinsa daga sharrin kawunanmu da munanan ayyuakanmu. Hakika Wanda Allah ya shiryar Babu Mai 6atar dashi, Wanda ya 6atar Kuma Babu mai shiryar dashi. Kuma Ina Shaidawa babu abinda bautawa da Gaskiya sai Allah shi kadai, kuma ba shi da abokin tarayya. Kuma Ina Shaidawa Muhammad bawansa ne Kuma manzonsa ne._

_Bayan haka, yan uwana kuma iyayena mata, wannan lekca ce wanda wasu bayanai ne wanda ya kamata ace na dan taba a yau ko Allah zai sa wasunku su gane. Wato yan mata kunada wasu matsaloli wanda kuma baku daukeshi a bakin komai ba. Matsala ta farko shine bakwa neman za6in Allah akan mijin da zaku aura, gaskiya al'amari wannan babban kuskure ne da wasu yan mata balagaggu sukeyi a yanzu. Saboda haka ki kasance mai yawan neman zabin Allah akan dukkanin al'amuranki musamman ga mijin da zaki aura._

_Matsala ta biyu kuma shine, idan aka samu wasu daga cikinsu suna neman za6in Allah, tho sai kuga suna addu'a akan Allah ya bani wane, wallahi yar uwa babban kuskure ne ki roki Allah ya baki wane koda kuwa yana da hali me kyau, saboda ba lallai kinsan internal dinshi ba, domin wasu mazan Masha Allah nagari ne, amma idan kika nace acikin addu'o'inki cewa Allah ya bani shi, Allah ya bani shi, tho zai iya zamo duk nagartarsa tho ba alkhairi bane a wajenki ba, saboda haka ki dage da rokon Allah yayi miki za6i na alkhairi domin Allah ya fimu sanin mafi alkhairin abu a garemu. Ina fatar kin fahimta? Amma babu laifi don kince ya Allah idan wane shine mafi alkhairi ka bani, tho wannan babu laifi, amma kuskure ne ki nace cewa Allah ya baki wane, Allah ya mallaka miki wane, saboda haka ku daina babu kyau._

_Rashin kula da wannan yasa zakuji wasu matan idan suka auri wanda suka nace acikin addu'o'insu cewa Allah ya basu, tho idan Allah ya basu sai suga kwata-kwata wannan halin nashi nagarin an nema an rasa, saboda me? Saboda ba shine alkhairi a wajanki ba._

_Matsala ta uku shine wasu yan matan yanzu basa dubiya izuwa ga namiji mai hali nagari mai hankali, wasu matan suna dubiya ne izuwa ga abin duniyan da ya tara. Jama'a hakane? Kuma wallahi wannan ba karamin kuskure bane babba, amma idan kunaso ku tabbatar da haka, tho kuje ku tambayi wadanda suka auri wani dan kudinsa kuji irin wulakanci da suke sha a zamantakewar._

_Jama'a wallahi acikin kashi 100% na matan aure, tho kashi 65% acikinsu suna fama matsaloli na zamantakewar aure, saboda haka jama'a mu dinga taya yan uwanmu mata addu'a, Allah ya basu zaman lafiya. Ya Ubangiji idan akwai wacce ta riga ta fada hannun dan iska mara tausayi, tho ya Allah ka shiryeshi ya zama nagari, ya Allah ka bashi ikon kyautatawa matarsa, ya Allah wadanda suke nema Allah Ubangiji ya hadasu da nagari, wacce ta riga ta kamu da son dan iska, ya Ubangiji ka shiryar dashi ya zama nagari, Ya Rabbi ka taimaki yan uwanmu, ka basu hakuri da juriya a zamantakewar su. Allah Ubangiji ya shiga cikin lamuranku._

_Jama'a akwai bukatuwar mu dinga yiwa iyayen mu mata addu'a, akwai wasu masu cewa Allah ya hada yar iska da dan iska, gaskiya al'amari wannan ba dai-dai bane, ka roki Allah ya shiryar dasu, ka roki Allah ya hada nagari da nagari, wadanda ba nagari ba, Allah ya shiryar dasu su zama nagari, amma ba dai-dai bane fadin haka. Sannan akwai wasu irin mutanen da suke cewa duk sadda mace tacewa saurayinta cewa Allah ya za6a mana mafi alkhairi, tho fah bata sonshi, tho wallahi wannan karyane, tana sonshi kawai dai alkhairinsa yake nema a wajen Allah. Saboda haka ku dage da neman za6in Allah a dukkanin al'amuranku._

_Matsala ta hudu shine gina soyayarku da karya, wallahi jama'a wannan ma babban matsala ne, dayawan matan mu sun fiya karyar tsiya a zance, acikin kashi 100% na yan mata, tho kashi 80% acikinsu karya kawai sukeyi a wajan tadi, musamman idan suka hadu da dan karya, saboda haka jama'a mu rage yin karya acikin soyayya, wallahi karya tana haifar da abubuwan dayawa na marasa kyau a zamantakewar aure. Saboda haka ku kiyaye._

_Allah Ubangiji yayi mana za6i mafi alkhairi, ya bamu zaman lafiya a gidajenmu, ya karemu daga dukkanin abin sharri._
=
=
_Dan uwanku a musulunci_
°
*_✍Abdulrasheed Ibn Musa Abms_*
°
°
.
Allah ta'ala yasa mudace
.
.
https://www.facebook.com/Zauren-Majalis-Sunnah-420869088334488/?referrer=whatsapp
.
ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.
Post a Comment (0)