*MAKARANTAR AZUMI 004//*
📌 ```ABUNDA AZUMI YAKE ZAMA WAJIBI DASHI```
Azumin Ramadana yana zama Wajibi ne da ɗayan abubuwa guda biyu:
1- Ganin sabon Jinjirin Wata; saboda faɗar Allah ( *(Cikin ku duk wanda ya halarci Watan Ramadan, to lallai ya azumce shi))* da faɗar Annabi SAW “ _Ku_ _ɗauki Azumi idan anga Wata, kuma ku ajiye Azumi idan an sake ganin wanin Watan_ ” [Bukhaariy da Muslim, daga Abu Hurairah].
A samu shaidawar mutane biyu Musulmai, mutanen kirki, amintattu, kuma ba sharaɗi bane sai dole mutum ya gani da idon sa sannan zai ɗauka.
2- A samu ɓoyewar jinjirin watan a ranar da aka neme shi, shine kamar a samu jido ko hadari ya lullube shi, to sai a cika lissafin Watan Sha’aban yakai talatin (30), kamar yadda ya tabbata cikin Hadisin da ya gabata.
i. Kuma sannan ganin Watan sauran Al’ummar Musulmi da suke wasu garuruwan, ya wadaci gaba-ɗayansu, kamar yadda Hadisin da aka ambata yake nunawa.
ii. Malamai sukace; Hadisin yazo ne yana Magana da dukkanin al’ummar Musulmi, ba wai wani ɓangare ba, ya zama Wajibi duk sauran al’umma su gudanu akan haka suyi aiki dashi, saboda abunda ke ciki na bin umarnin Annabi SAW.
iii. Sannan kuma har wayau shi zai samar da haɗuwar kan al’ummar Musulmi, kamar yadda ake iya ganin a sauran Watanni, kamar Watan Zhul-Hijjah bai yiwuwa a samu irin wannan shan bamban ɗin.
✍ *ANNASIHA TV*
*Twitter* 👇
https://twitter.com/AnnasihaTv?s=09
*Telegram* 👇
https://t.me/AnnasihaTvChannel