Menene Memory Card Da Yadda Ake Dawo Da Abubuwan Da Aka Gogesu Acikinsa (Formated or Deleted). Kashi na farko (1).
Daga: Salisu Abdulrazak Saheel
Daya daga cikin tambayoyin da jama'a sukeyi kenan, ko jiya mutum ukku sunkirani sunamin irin wannan tambayar.
Ya mutum zaiyi ya dawo da kayan dake cikin wayarsa idan ya rasa kayan dake cikin ma'ajin kayayyakin wayarsa (Memory card)..?
Amma kafin na fadi yadda ake dawo da kayan da aka rasa acikin ma'ajin kayayyakin waya (Memory card) yanada kyau na sanarwa jama'a yadda shi Memory card din yake da kuma irin kulawar da yake buqata idan ka mallake shi..
Memory dai wani irin mazubi ne da akayi shi domin ya baiwa mutane damar ajiyar kayayyakin da akayi su da wutar lantarki (Electronic Data) wanda sune kamar haka: Hotuna, rubutu, hoto mai motsi (Videos), waqoqi da duk wani abinda akan iya adana shi acikin Computer.
Wato shi dai memory yanada yanayi mabanbanta dangane da yadda akeyinsa, da kuma tsarin yinsa, sai dai mafi shahara acikinsa shine wanda akeyin amfani dashi a mafi yawan wayoyin "tafi da gidanka" na zamani a baya, mafi yawan kamfanonin da suke kirkirar wayoyi da Cameras kowa da irin yadda yakeyin nasa Memory din ta wajen bangaren girmansa ko fadinsa wanda hakan yasa ake samun matsala sai kaga memorin wani kamfanin baya aiki a wata na'ura da ba tasa ba.
Amma bayan da waya kirar "Android" tasamu karbuwa sosai a duniya sai ya zamana sun samu hadin kai wurin tabbatar da Mazubin "Memory" ya zama yanada rami iri daya wanda zaizama kowace waya ko "Tablet" zatayi amfani dasu.
A baya "Memory" yanada tsada matika, gashi kuma a lokacin yana matiqar wahalar samuwa a kasashenmu, gashi kuma bashida girma wurin kwasar bayanai.
Amma Alhamdulillah yanzu wannan babu shi domin a yanzu akan iya samun "Memory" wanda a kalla yana iya daukar Gig dubu (GB-1000) shi kadai..
Daga cikin abinda yake damun jama'a shine: yawan lalacewarsa sannan kuma yakan lalata abubuwan dake cikinsa (Currupted).
Mutane da dama suna manta cewa "Memory" shima kayan Computer ne kuma yana iya lalacewa kowane lokaci musamman idan baka kulawa dashi yanda yakamata ba, wani lokaci bawai "Memory" yana lalacewa bane, sometimes ana samun matsala a wurin da aka sakashi ne.
Misali: Zai iya yiwuwa kasamu wayar da take dauke da "Memory" da yake da tsarin ajiyar bayanai na (File Alocated Table) FAT.
To idan kasaka shi acikin wata wayar da bata daukar wannan tsarin to sai kaga ta rubuta maka cewar: Wannan "Memory" yayi dameji.
Kokuma ma wani lokaci zakaga duk abinda ke cikin "Memory" din yaki budewa kokuma ya nuna alamar lalacewa wanda kuma nuna hakan bashine alamun cewa "Memory" din ya lalace ba zata yiwu shima yanada dangantaka da irin "File System" din da aka ajiye kayan tun farko.
Wani lokaci kuma zakaga ka dauko kaya daga cikin Computer ko wata wayar amma da zaran ka tashi budewa sai kaga yana fada maka cewar: "Unsupported Format" to wannan ma ba yana nufin cewa "Memory" din ya lalace bane yana nufin cewa wayar batada Application din da zai bude.
Duk wannan dai bashi ne abinda zanyi maku bayani ba, amma dai yanada kyau kusan hakan..
To yanzu idan kayi Mistake kayi formatting wayarka kuma kanaso kadawo da kayan da ka goge to kabi wannan matakan domin dawo dasu: a tsari irin na bature da kuma yadda yayi kayan ajiya na Computer wato "Storage Devices" yanada kyau jama'a sunsan cewa duk abinda yataba shiga cikin "Memory" na Computer ko na waya, ko na Flash har abada yananan koda kuwa angogeshi kokuma ma anyi Formatting to lallai yananan kuma za'a iya dawo dashi.
Hanyoyin dawo da kayayyakin da karasa a memory dinka sunada yawa: akwai Tayin amfani da shafukan internet domin samun biyan buqata amma a nawa shawarar bancika son jama'a suna amfani da wasu shafukan internet ba wurin yin irin wannan aikin ba, kasancewar yawancin wasu shafunkan a internet na yaudara ne da yan damfara da kuma masu zubawa mutane Miyagun Virus, cikin wayarka kokuma Computer dinka amma akwai na kirki sai dai mafi yawansu sai kabiya kudi.
Amma yau insha Allah zan nuna mana wasu Manhajoji (Software) na computer wadanda kyauta ne kuma garanti ne ga duk wanda yakeson yayi amfani dasu wajen dawo da kayan da ya rasa.
Farko: idan "Memory" dinka yana cikin Computer ne kuma baya nuna "Memory" to kaciro shi ka sakashi a cikin "Card Reader" domin fara yin wannan aiki.
Abun kiyayewa shine tunda da Computer zakayi wannan gyara to kasani mafi yawan Computers da muke amfani dasu a wannan kasar tamu kashi 60% suna dauke da Virus mai cinye kayan Computer ya mayar dasu "Shortcuts" to gaskiya amfani da irin wannan Computer din akwai hatsari, saboda haka kasamu Computer da kasan tanada "Anti-Virus" mai kyau kuma ana Updating dinsa kafin ka zura memory dinka.
Idan kasan akwai wadansu kaya acikin "Memory" din to yanada kyau ka kwashesu ka zubasu acikin wani "Folder" domin kada garin so kadawo da abubuwan da karasa ya zama kuma sunada suna iri daya da kayan dake cikin "Memory" din, kaga zasu dawo su hau saman wadanda keda suna irin nasu kenan..
Ga manhajojin (Software-Application) da zaka zaba kadauka domin dawo da abinda ka rasa:
1. Recuva (na aiki a windows ne kawai).
Wannan Application na "Recuva" (Version 1.5) nauyin sa 4.02MB ne kuma kyauta ne, yana aiki a Computer din da takeda "Operating System" na "Windows" ana kuma iya sakashi a "Windows 2000" zuwa sama.
Idan kanaso ka dawo da "FILES" din da ke cikin "Memory" dinka to zaka saka "Memory" din cikin "Card Reader" sannan se ka zurashi acikin Computer sai kayi Installing wannan "App" din na "Recuva"
Sai kayi Clicking din "Recuva" din sai ka zabi shi "Memory" din acikin jerin manyan kwakwalen da suke jikin Computer din sannan sai ka taba "Scan".
Daganan zaka bashi lokaci dan zai dawo da kayan da aka goge, sannan zai baka "Recover" sai ka tabashi domin yadawo maka da wadanda kakeso.😀
2. "Pandora Recovery" (Yana aiki a Windows ne kawai)
"Pandora Recovery" shima kyauta ne yanada girman: 3.12.MB, yana aiki a Computer da akasa mata "Windows" kuma wacce "Operating System" dinta yafara da "Windows XP" zuwa sama.
Shima zakabi process din da akabi wurin aiki da "Recuva" ne.
Sai dai shi zakaga "Qick Scan" da kuma "Deep Scan".
Shi "Quick Scan" ga wanda yakeson dawo da abubuwan da yayi "Deleting" amma wanda yayi "Formating" to shi zaiyi Amfani da " Deep Scan" ne.
Bayan kagama zai baka Option:
1. Kodai kayi amfani da "Pandora Recovery Wizard" wanda zai dinga baka su daya bayan daya kana zaba kana fito da wanda kakeso.
2. Kokuma kayi Right Click ka zabi abinda kakeson ka dawo dasu.
Alhamdulillah..
Mu hadu kashi na (2)
Allah yabada sa'a..
08137350232 Whatssp Only..