TAMBAYA TA 52


*Tambaya*

Assalama Alaik, Malam
meye hukuncin Wanda ake binsa azumin ramadan, kuma Ga Shawwal zai wuce, shin ya halasta mutum yayi sitta Shawwal kafin ya biya ramadan

AMSA
Wa alaikumussalaam Wa Rahmatullahi Wa Barakaatuh.
Farko dai mafi yawan mallamai sun tafi a kan wanda ya ke da ramuwa a kanshi abin da ya fi dacewa shine ya fara yin azumin da ake binshi, amma yayin da lokaci ya kure mishi na yin ramuwan ko kuma yana da ramuwa da yawa sanadiyyar wata lalura kamar rashin lafiya ko jinin al-ada ko jinin biki,ko makamancin hakan idan yace zai rama su kila watan Shawwal zai fita ba tare da ya kammala su ba har yasamu daman yin azumin sittu Shawwal ko kuma wani jinin zai iya zuwa wa mace kafin ta gama ramuwar kuma tayi sittu Shawwal din to mallamai sun yi maganganu kamar haka:

(1) Sa'id Ibnu Jubair da Abu Hanifah da riwayah daga Al-Imamu Ahmad( Allah Ya jikansu da Rahamar Shi) suna ganin halascin mutum zai iya yin sittu Shawwal ko dukkan wani azumin nafila kafin ya yi azumin ramuwar Ramadan dake kan shi, kuma shine zahirin ra'ayin A'ishah Allah Ya kara mata yadda. Daga cikin dalilan su fadin Allah(SWT) cikin Suratul Bakarah 
(فمن كان منكم مريضا أو على سفر فعدة من أيام أخر)
"Wato wanda ya
kasance daga gareku majinyaci ko akan hanya ta tafiya bai samu daman yin azumi ba sai ya biya(ya rama) a wasu kwanuka na daban."
A nan Allah(SWT) ,Ya yi bayanin kowane lokaci kuma kowane wata mutum zai iya rama su.Haka hadisi ya tabbata cikin Sahihul Bukhari da Sahihu Muslim da Sunanuttirmiziyyi daga Aisha(Allah Ya kara mata Yadda) tace
كان يكون علي الصيام من رمضان فما أستطيع أن أقضيه إلا في شعبان
A'ishatu (Allah Ya kara mata Yadda) take cewa 'Wani lokaci zai kasance ana bina bashin ramuwar azumin Ramadan bana iya biyan su sai a watan Sha'aban, wannan ya ke nuna tana yin azumin nafiloli duk da cewa akwai bashin ramuwa a kan ta, sannan suka kara kafa hujja da cewa wasu azumin nafiloli an sanya musu lokuta wanda duk wanda yake so ya yi su to dole zai yi su a wadannan lokutan ne, sabanin ramuwa mutum zai iya yin su a kowane lokaci, kamar yadda muka yi bayani karkashin waccan Ãyar.

(2) Wadanda suke ganin mutum ba zai yi sittu Shawwal ba sai ya rama azumin Ramadan dake kan shi. Daga cikin dalilan su hadisin manzon Allah (SAW) wanda Al-Imamu Muslim da Abu Dawood da Tirmiziyyi da Ibnu Maajah da Nasaa'i suka fitar cikin littattafan su daga Ayyub ya ce
(من صام رمضان ثم أتبعة ستا من شوال فذلك صيام الدهر),
'Wato wanda Yayi azumin Ramadan sannan ya yi sittu Shawwal kamar yayi azumin zamani ne'.
Suka ce a nan Annabi (SAW) ya yi isharan sai mutum ya yi duka azumin Ramadan sannan zai yi sittu Shawwal. Sannan 
Al-Imamu Malik ya kyamaci mutum ya yi azumin nafila kafin ya biya azumin ramuwar Ramadan dake kan shi, haka riwayah daga Al-Imamu Ahmad yana ganin hakan bai halasta ba, haka Al-Imamushshafi'i ya fifita mutum ya fara biyan azumin ramuwan Ramadan shi yafi dacewa kafin nafilah.

FADAKARWA: Wasu mallamai sun rinjayar da ra'ayin farko wasu kuma sun rinjayar da ra'ayi na biyu, amma domin fita daga sabanin mallamai abin da ya fi dacewa mutum yayi kokari ya fara biyan ramuwar da ke kan shi na Ramadan sannan sai yayi sittu Shawwal, amma idan lokaci ya kure mishi ko kuma ramuwar da yawa ba zai yiwu ya hada su ba to babu laifi ya dau ra'ayin farko na mallamai wato ya fara yin sittu Shawwal sannan daga baya sai yayi ramuwar dake kan shi.
والله تعالى أعلم.

DR NASIR YAHYA ABUBAKAR BIRNIN GWARI

2ND JUNE 2020

Daga 
*MIFTAHUL ILMI*

Ku Danna link din dake Qasa don kasancewa damu a shafin telegram👇
https://t.me/miftahul_ilmi

→Ga masu sha'awar shiga miftahul ilmi a WhatsApp sai su shiga ta nan su aika da cikakken suna 👇
https://wa.me/2347036073248
Post a Comment (0)